Addini

Dr. Zakir Naik ya baiwa Falasɗinawa kyautar kudi miliyan 383M

Fitaccen malamin addinin musulunci Dr zakir Naik wanda ya shigo kasar Nijeriya a jihar Sokoto wajen da’awa kamar yadda ya saba inda inda yanzu haka yake gabatar da lakca a dakin babban taro na jihar Sokoto ta ke kasarawa.

Kamar yadda wani matashin malami a nan najeriya ya wallafa cewa Abdul-hadee isah ibraheem ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda yake fadin wani babban alkhairi da wannan babban malamin yayi Allah ya saka masa da aljannah.

'Dr. Zakir Naik ya baiwa Falasɗinawa kyautar kudi miliyan 380Millon
Dr. Zakir Naik ya baiwa Falasɗinawa kyautar kudi miliyan 380Millon

Kai tsaye daga wajen lakcar da Dr Zakir Naik yake gabatarwa yanzu haka a Sokoto. Yace:

“Wasu ‘yan siyasa guda biyar sun ɓata min suna, kuma na maka su a kotu. Mun sasanta da huɗu, amma na biyar ɗin kam na ki amincewa mu sasanta. Bayan tsawon lokaci ana Shari’a, yau da safe, 2 ga watan November, an yanke hukunci. Alkali ya umarce shi ya biya ni kuɗi akan ɓata min suna da yayi, kuɗin na idan an canza zuwa kudin Nigeria, yana daidai na Naira miliyan ɗari uku da tamanin da uku! Ku shaida na sadaukar da kudin ga Falasɗinawa. Ba na buƙatan ko sisi a ciki!”

Bawan Allah, Allah ya biya ka, ya karba maka aiyukan ka, ya ‘kara daukaka fiye da yadda Makiya suke zaton ka kai.

Ga bidiyon nan inda yake fadi da bakinsa.







Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button