Labarai

Dan keke Napep : Ya Tsinchi Naira Milyan Tara 9 Million Ya Maidawa Mai Shi a Jihar Yobe

Advertisment

A yau din nan majiyarmu ta samu wani Kyakykyawan labari wanda tabbas wannan matashi yayi abun bajinta da ya kamata a jinjina masa irin wannan gudun abin duniya da haram na mayar da kudi duk da ana cikin tsananin farata da yunda da tsadar rayuwa.

Wani ma’aboci mai amfani da kafar sada zumunta Jauro Ahmad ya ruwaito wannan labari a shafinsa na sada zumunta inda wani matashi yayi abin kokari inda yake cewa.

“Wannan shine Ari Bulama Aji (Ari Luu) Mai Sana’ar Achaba Da Tsohuwar NAPEP Dake Garin Jumbam , Karamar Hukumar Tarmuwa A Jahar Yobe, Wanda Ya Tsinchi Kudi Har Naira Miliyan Tara

Dan keke Napep : Ya Tsinchi Naira Milyan Tara 9 Million Ya Maidawa Mai Shi a Jihar Yobe
Dan keke Napep : Ya Tsinchi Naira Milyan Tara 9 Million Ya Maidawa Mai Shi a Jihar Yobe

Ba Tare Da Bata Lokaci Ba Ya Mayar Da Kudin Da Ya Tsinta

Lamarin Ya Faru Ne Sati Daya Gabata (17/11/2023)

Allah Ya Kara Mana Irinsa A Chikin Alummah.”

Wani labari: Wani matashi Dan Sahu ‘keke napep’ ya Maida kudi Miliyan 15 da ya tsinta

Wani matashi dake tuka Babur din Adaidaita Sahun mai suna Auwalu Salisu Wanda aka fi Sani da Na Baba dake bayan tashar Yan Kaba, ya dawo da wasu kudi Mallakin Alhaji Ibrahim Barka Daga kasar Chadi da aka manta a babur dinsa ranar Alhamis din data gabata.

Kudin akwai Saifa Milyan 10 da Dubu 130 sai kuma sama da Naira Milyan 2 biyo bayan jin sanarwar cigiyar kudin a tashar Arewa Radio 93.1.

Daga karshe an bashi tukuichin tsintuwa har Naira Dubu ‘Dari 400.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button