Labarai

Dalilan da suka sanya kotun daukaka kara ta tabbatar da Gawuna a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano – Abba hikima

A jiya juma’a 17/11/2023 kotun daukaka kara ta yanke hukunci akan zaben jihar kano tsakanin Dr. Nasiru Yusuf gawuna da kuma engr. Abba kabir yusuf (abba gida gida) wanda shine yanzu haka akan karagar mulki jihar kano.

Kwanan baya kotun sauraren kararaki ta tabbatar da Dr.nasiru yusuf gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben jihar kotu bayan da an zaftare kuri’un abba kabir yusuf 165,000 da yan kai.

Barrister Abba hikima ya samu halarta zaman kotu jiya inda ya bayyanawa dcnews hausa dalilin da ya sanya kotu ta ayya dr.nasiru yusuf gawuna dan Jam’iyar Apc a matsayin shine zaɓaɓɓen gwamna jihar kano.

“Abubuwa gudu takwas anka gabatar a wannan kotu amma uku sune manya manya a ciki na farko shine

Rasa sanya sunan dr.nasiru Yusuf gawuna a cikin wannan ƙara wanda kotu tace wannan ba matsala bane ba, inda ta bada hujja aka dokar electoral act ta fadi cewa shi dan takara ko jami’ya suna iya sanya ƙara tare ko daban daban da wannan tayi amfani ta ƙori wannan gabar.

Na biyu: magana ce akan hukunci da aka bayar ta yanar gizo “zoom” kenan aka tambayi kotu koda ya saɓawa sassan kundin tsarin nijeriya wanda yake bukatar lallae bai zamo “public hearing” akan bukace bukacen tsare-tsaren nijeriya , nan ma kotu ta fadi cewa babu wani abu da ankayi na rashin adalci “injustice” wajen karatu wannan hukunci a yanar gizo domin jama’a sun fahimci abinda ake nufi da hukuncin.

Sai kuma na ukku: wanda yake da ɗan girma ko yafi kowane girma fassara da kotun daukaka kara ta bayar akan sashi na 177 na tsarin mulkin nijeriya,wanda a ciki ake cewa, kafin mutum ya cancanta ya tsaya takarar gwamna a kowa ce jiha a nijeriya wanda sai ya zamo aka kawo ƙa’idoji ilimi, shekaru da sauransu, wanda shine mai muhimmanci a gaban kotu sai ya zamo dan jam’iya ne, akwai jam’iya da yake cikinta sa’a nan yayi takara a cikinta.

Sa’a nan kuma sai jami’ya ta dauki nauyin tsayar da shi a cikin wannan muƙami , to a cikin wannan ne kotu tayi amfani tayi wani hukunci da ita Kotun kasa “tribunal” kenan tayi inda take cewa ta duba cikin rigista ‘ya’yan jam’iyar NNPP kenan wanda aka gabatar a kasa, kuma bata samu sunan gwamnan kano mai ci yanzu Abba kabir Yusuf , babu sunansa a ciki, amma sai tribunal tayi gaba tana cewa ba hurumin ta bane saboda babu sunansa tace bai cancanta ba sai tayi amfani da hukuncin APM da inec a kasa kenan a tribunal.

To ita kuma kotun daukaka kara tace tunda dai kotun “tribunal” ta gano cewa babu sunan abba kabir Yusuf a cikin ‘ya’yan wannan jami’ya to akwai wajibci ma akan wacan kotun ta farko tayi gaba ta fadi cewa bai cika wannan bukace bukace na wannan shashi ba na 177 bai cancanta ya tsaya takara ba a jihar Kano, bai cika wannan sharuda na tsayawa takara ba, saboda wanda wannan tsarin mulkin nijeriya ya kawo su, to wannan shine a takaice abinda kotun ta fadi ta kori wannan karar.

Ga bidiyon nan ku saurara sauran bayyanai.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button