Dakarun tsaron Najeriya sun aika Ƴan ta’adda 99 barzahu,sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro
![Dakarun tsaron Najeriya sun aika Ƴan ta’adda 99 barzahu,sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/11/FB_IMG_1700832677028.jpg?fit=960%2C492&ssl=1)
![Dakarun tsaron Najeriya sun aika Ƴan ta’adda 99 barzahu,sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/11/FB_IMG_1700832677028.jpg?fit=960%2C492&ssl=1)
Hedikwatar tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa a cikin makon da ya gabata sojin Najeriya sun kashe ƴan ta’adda 99 kuma sun kama wasu 198 a Najeriya.
Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis a Abuja.
Buba ya ce jami’an tsaron sun ceto mutum 139 da aka yi garkuwa da su sun kuma kama bindigogi 141 da harsasai 1,463 a yankin Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.
Ya ce makaman da dakarun suka kama sun hada da bindiga GPMG daya, GT3 daya, AK47 guda 49, Josef Magnum Pump Action daya, double barrel daya da single barrel biyu, tashar Liberty Tvr na ruwaito.
![Dakarun tsaron Najeriya sun aika Ƴan ta’adda 99 barzahu,sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro Dakarun tsaron Najeriya sun aika Ƴan ta’adda 99 barzahu,sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/11/FB_IMG_1700832677028.jpg?resize=300%2C154&ssl=1)
![Dakarun tsaron Najeriya sun aika Ƴan ta’adda 99 barzahu,sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro Dakarun tsaron Najeriya sun aika Ƴan ta’adda 99 barzahu,sun kama wasu 198 – Hedikwatar tsaro](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2023/11/FB_IMG_1700832677028.jpg?resize=300%2C154&ssl=1)
Saura sun hada da pistol kiran hannu 9, bindigan mafarauta 13, hand grenade – 1, manyan bindigogi kirar hannu -7 da grenade kirar hannu 2.
A Arewa maso Gabas Buba ya ce rundunar ‘Operation Hadin Kai’ a ranar 17 ga Nuwamba sun kama mutum uku da ake zargin masu hada baki da mahara a karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Dakarun sun kama mutanen yayin da suka je karbo sako wa maharan.
Ya ce ‘yan ta’adda 108 da iyalen su da suka hada da maza 23, mata 32 da yara 63 sun mika wuya ranar 17 da 23 ga Nuwamba.
Dakarun sun kashe mahara 19, sun kama 21 sun kuma ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su a yankin.
A Arewa ta Tsakiya Buba ya ce rundunar ‘Operation Safe Haven’ sun kashe ‘yan bindiga uku, sun kama 32 sannan sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su.
Dakarun sun kama bindigogi, harsasai a mabuyar maharan.
Ya ce rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ sun kashe ‘yan ta’adda biyu, sun kama wasu guda 9 sannan sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a kananan hukumomin Takum da Katsina-Ala dake jihohin Benuwe da Taraba.
Dakarun sun kama makamai da su ka hada da AK47 -1 da harsasai 28.
A Arewa maso Yamma Buba ya ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe ‘yan bindiga 20, sun kama wasu 20 Kuma sun ceto mutum 83 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara.
Ya ce rundunar sojin sama ta yi wa gidan shahararren dan bindiga Lalbi Nagogo ruwan bama-bamai a karamar hukumar Danmusa dake jihar Katsina bayan sun samu labarin cewa yana wurin tare da sojojinsa.
Buba ya ce rundunar ‘Operation Whirl Punch’ sun kashe ‘yan ta’adda 16, sun kama 16 Kuma sun ceto mutum 3 da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna da gundunmar Kuje dake Abuja.
Buba ya ce a ranar 16 ga Nuwamba rundunar sojin sama ta yi wa wani Shugaban ‘yan bindiga Boderi ruwan bama-bamai a maboyarsa dake karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.