Ciyaman din karamar hukumar Lokoja ya faɗi ya rai yayi halinsa


Shugaban Karamar Hukumar Lokoja, Hon. Mohammed Danasabe Muhammad, ya rasu.
Daily Trust ta rawaito cewa an tabbatar da rasuwarsa da misalin karfe 4:30 na safe a wani asibiti da ke Lokoja babban birnin jihar.


An garzaya da Muhammed asibiti bayan da ya faɗi a gidansa.
An ce ya halasci tarurrukan siyasa ne na shirye-shiryen zaben gwamnan da za a yi a gobe Asabar.
Wata majiya daga dangin mamacin ta ce an garzaya da shi asibitin Shifa, Lokoja, jim kadan bayan ya rufta a gidan da yammacin ranar Alhamis.
“Likitoci sun tabbatar da mutuwarsa a asibiti da misalin karfe 4:30 na safiyar ranar Juma’a,” in ji wani dangin da ya nemi a sakaya sunansa.
Marigayin ya fito ne daga mazabar B dake yankin Lokoja.
Za a yi jana’izarsa a makabartar Musulmi ta Unguwan Kura bayan sallar Juma’a.