Labarai

Buri na shine in ga mutum sama da miliyan ɗaya sun samu ilimi ƙarkashi na kafin in koma ga Allah – Farfesa Gwarzo

Gogarman tabbatar da kowa ya samu ilimi musamman, ƴaƴan talakawa a Najeriya da ma kasashen waje, farfesa Adamu Gwarzo ya bayyana cewa burin sa shine ya ga akalla yara sama da miliyan ɗaya sun samu ilimi a faɗin kasar nan.babba jaridar watsa labarai premium times na ruwaito.

Burin farfesa Gwarzo shine ya tabbata Ilimi ya wanzu a ko’ina a faɗin ƙasar nan.

Buri na shine in ga mutum sama da miliyan ɗaya sun samu ilimi ƙarkashi na kafin in koma ga Allah – Farfesa Gwarzo
Buri na shine in ga mutum sama da miliyan ɗaya sun samu ilimi ƙarkashi na kafin in koma ga Allah – Farfesa Gwarzo

Da yake jawabi a lokacin da yake tabbatar da soma karatu a jami’ar Canada dake Abuja, wanda ɗaya ne daga cikin jami’o’in da ya kada a Najeriya, Farfesa Gwarzo yace cikin shekarar 2024, za a fara karatu gadangadan a wannan jami’a.

” Jami’an Canada za ta fara karatu daga shekarar 2024. Muna zangon karshe na kammala ayyuka a jami’ar domin soma karatu.

Farfesa Gwarzo ya kafa jami’o’i 4 a ƙasar nan da jamhuriyar Nijar wanda dukkan su suna aiki.

Wani Labari :Kwankwasiyya : Sama da mata dubu daya sunka yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a kano

Kimanin mata sama da dubu daya ne suka gudanar da zanga-zanga a titunan Kano domin nuna damuwarsu kan cece-kucen da kotun daukaka kara ta yi, shafin gidan rediyo nasara radio fm na ruwaito.

Matan dauke da alluna suna rera wakokin goyon bayan gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf sun tunkari rundunar ‘yan sandan jihar inda suka mika takarda dauke da korafe-korafensu kan sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Wannan shi ne karo na farko a tarihin Kano da mata suka zo da jama’a don yin maci kan tituna suna neman a yi wa dimokradiyya adalci tare da kare wa’adin zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button