Labarai

Bola tinubu zai siya wa kan sa jirgin ruwan shaƙatawa na Naira biliyan 5, kimanin adadin kuɗaɗen da zai bai wa ɗaliban jami’o’i bashi

Shugaba Bola Tinubu ya ware wa kan sa Naira biliyan 5 domin sayen jirgin ruwan Shugaban Ƙasa, yayin da ya ware Naira biliyan 5.5 domin rabawa ga ɗaliban jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare na ƙasar nan.

Wannan adadin na daga cikin toliyar Kasafin 2023, wanda Tinubu ya aika Majalisar Dattawa domin ta amince cikin gaggawa, majiyarmu ta Leadership hausa na ruwaito.

Sannan kuma a ciki akwai Naira biliyan 5.1 da za a kashe wajen gyaran makarantu 100 a cikin kwanaki 100 a Gundumar FCT, Abuja.

Bola tinubu zai siya wa kan sa jirgin ruwan shaƙatawa na Naira biliyan 5, kimanin adadin kuɗaɗen da zai bai wa ɗaliban jami’o’i bashi
Bola tinubu zai siya wa kan sa jirgin ruwan shaƙatawa na Naira biliyan 5, kimanin adadin kuɗaɗen da zai bai wa ɗaliban jami’o’i bashi

Sai dai kuma ana ta suka da ƙorafi kan kasafin, bayan Tinubu ya ware Naira biliyan 28 domin sayen motocin alfarma na Ofishin Shugaban Ƙasa, na Uwargidan sa Remi da kuma gyaran gidan shugaban ƙasa da sauran wasu ayyukan biliyoyin kuɗaɗe a Fadar Shugaban Ƙasa.

Haka kuma kasafin ya nuna duk da kukan matsalar rashin kuɗi, Tinubu zai kashe wa Jiragen Shugaban Ƙasa Naira biliyan 12.

Sannan kuma za a kashe Naira biliyan 4 domin yi wa gidan Shugaban Ƙasa kwaskwarima.

Shi ma gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, za a kashe masa Naira biliyan 2.5 domin yi masa kwaskwarima.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa, duk da kukan rashin kuɗi, Tinubu zai gwangwaje Remi matar sa da motocin Naira biliyan 1.5, shi ma zai sauya motocin ofishin sa da Naira biliyan 2.9.

Duk da matsalar rashin kuɗi da tsadar rayuwar da ake ta kuka, wadda gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ya jefa ‘yan Najeriya bayan cire tallafin fetur, Tinubu zai gwangwaje Remi matar sa da motocin Naira biliyan 1.5, shi ma zai sauya motocin ofishin sa da Naira biliyan 2.9.

Waɗannan Naira biliyan 2.9 kuwa, Gwamnatin Tinubu za ta kashe su ne wajen maye danƙara-danƙaran motocin Ofishin Shugaban Ƙasa, waɗanda aka ci zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

Wannan adadin kuɗaɗen su na cikin toliyar Kasafin 2023 na ƙarshen shekara, wanda Tinubu ya aika Majalisa domin amincewa.

Su na cikin kasafin na Naira tiriliyan 2.17 da ya aika Majalisar Dattawa a ranar Talata domin amincewa.

A ranar Litinin ce dai Majalisar Zartaswa ta ƙasa ta amince a kashe kuɗaɗen domin gaggauta aiwatar da wasu ayyuka masu matuƙar muhimmanci ga ƙasa.

Shugaba Tinubu da manyan jami’an gwamnatin sa har yau ba su daina roƙon ‘yan Najeriya su ƙara haƙuri da juriyar ɗanɗana raɗaɗin tsadar rayuwar da su ke fama ba, tun bayan rantsar da Tinubu, watanni biyar da suka gabata.

Nazarin kasafin da PREMIUM TIMES ta yi ya nuna gwamnatin Tinubu ta haukace tuburan wajen ragargazar maƙudan kuɗaɗen da ya kamata a yi wa ‘yan Najeriya ayyukan raya ƙasa da su. A gefe ɗaya kuma su na roƙon ‘yan Najeriya su ci gaba da sadaukar da kan su talauci da raɗaɗin tsadar rayuwa na ci gaba da kwankwatsar su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button