Bashin Da Najeriya Ta Ciyo Ya Karu Zuwa Tiriliyan N89.3
Bashin da ake bin Najeriya ya karu da Naira tiriliyan 20.6 a sakamakon faduwar darajar Naira a watanni biyar da Shugaba Tinubu ya yi a bisa mulki.
Aminiy a gano, a wata guda basukan da ake bin kasar suka karu zuwa Naira tiriliyan 89.2, duba da shirin gwamnatin na kara ciyo bashi daga kasashen waje.
Hakan na nufin bashin N418,779 ke kan kowane dan kasar mai yawan al’umma miliyan 13 jaridar aminiya hausa na ruwaito.
A watan Oktoba ne m Ministan Kudi, Wale Edu, ya sanar da shirin Gwamnatin Tarayya na ciyo bashin Dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya.
Idan bankin ya ba da bashin, abin da ake bin Najeriya zai karu zuwa Dala biliyan 114.9, wato Naira tiriliyan N89.2, a bisa farashin canjin Dala na N776.4.
Wannan kuma bai hada da shirin gwamnatin na karbo wani bashin na Dala biliyan 7.8 da kuma miliya €100m da Shugaba Tinubu ya samu sahalewar Majlisar Dattawa a matsayin wani bangare na kasafin 2022-2024.
Aminiya ta gano cewa ba don kara faduwar Darajar Naira daga N461 da CBN ke canjin Dala a ranar 30 ga watan Mayu ba, da jimillar bashin da ake bin kasar bai fi tiriliyan N57.6 ba.
Faduwar darajar Naira da 315 a wajen canjin Dala a cikin kwanaki 30 din ta sa bashin da ake bin Najeriya karuwa da da tiriliyan N20.6 zuwa tiriliyan 89.2.
Wasu daga basukan
Zuwa watan Yuni, bashin da kasar ta ciyo daga waje Dala biliyan 43.1 ne; na cikin gida Dala biliyan 70.3.
Kungiyoyin kasa da kasa suna bin ta Dala biliyan 20.7; kasashen waje na bin ta Dala biliya 5.5; sai Eurobon Dala biliyan 15.6; takardun amumin Dala miliyan 931 da wasu basukan na Dala miliyan 300.
Daga cikin basukwan kasashen waje na Dala biliyan 43.1, ana bin gwamnatin tarayya biliyan 38.8, jihohi da Birnin Tarayya Dala biliyan 4.3.
Jihohi mafiya cin bashi:
Jihohin da aka fi bi bashi a cikin Dala biliyan 4.3 su ne:
- Legas — Dala bilyan 1.2
- Kaduna — Dala miliyan 569
- Edo — Dala miliyan 258
- Bauchi — Dala miliyan 170
- Kuros Riba — Dala miliyan 153
Mafiya karancin bashi:
Wadanda bashinsu ya fi karanci su ne:
- Borno — Dala miliyan 18m
- Taraba — Dala miliyan 21
- Yobe — Dala miliyan 21
- Jigawa — Dala miliyan 26
- Binuwai — Dala miliyan 29
- Filato — Dala miliyan 31.