Labarai

Ba ranar daina amfani da tsoffin takardun Naira — Kotun Ƙoli

Kotun koli ta yanke hukuncin cewa tsoffi da sabbin takardun kudi na Naira za su kasance tare a matsayin halastattu har sai baba-ta-gani.

A watan Maris din 2023 ne kotun kolin ta kara wa’adin deba amfani da tsoffin takardun Naira na N200, N500 da N1000 har sai zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

A ranar 21 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban kotun koli, tana neman a kara wa’adin.

Daily Nigerian hausa na ruwaito a cikin sabuwar takardar da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Lateef Fagbemi, shigar, ya ce saboda matsalar tattalin arziki da ake fama da ita, babban bankin kasa ya kasa buga adadin sabbin takardun da za su taimaka wajen kawar da tsofaffin takardun kudaden kafin watan Disamba. 31.

Sai dai kuma a zaman kotun da aka yi a yau Laraba, tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin AGF, ta gabatar da bukatar.

Da ya ke zartar da hukuncin, kwamitin alkalai bakwai, karkashin jagorancin Inyang Okoro, ya ce za a ci gaba da amfani da duka tsofaffi da sabbin takardun N200, N500 da N1000, har sai gwamnatin tarayya ta gabatar da wani tsari bayan tuntubar masu ruwa da tsaki.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button