Abin da yasa na maka amdaz a kotu – – Alhaji Sheshe
A jiya ne daya daga cikin masu shirya fina finai Mustapha Ahmad Alhaji sheshe ya maka Abdallah Amdaz kotu inda ba’a wata wata ba tun jiya anka tura masa sammace kuma kamar yadda shi wanda anka kai ƙara ya fadi cewa tabbas ya karbi sammacin amma su sani idan za’a busa ƙaho bazai taɓa karya ta kanshi ba.
Mun kawo muku labarin maka shi kotun a nan Hausaloaded munka ce ƙari bayyani yana nan zuwa to yanzu shine munka samu zantawar shi alhaji sheshe da gidan rediyo Freedom Kano inda yake bayyana dalilin sanya wannan kara da yayi ga abinda yake cewa.
“Wannan matakin ni na dauke shi ne saboda ni bahaushe ne musulmi cikakken bakono , ban ma san dagina ba bayan Kano, iyali na suna da mutunci, ina da mutunci a cikin iyalina da unguwa ta da Masana’ata ta shirya fina finai.
Bayan ni nasan bana daga cikin masu saɓawa ƙa’idar fim a Kano kuma bana daga cikin waɗanda suke saɓawa addini na wajen gudanar da shirya fina finai na, bana daga cikin mai nuna aibun gwamnati ko wata kabila.
Amma haka kawai wani mutum yazo yayi mana kuɗi goro yace mana yan iska, waɗanda suke aikata ba daidai ba a gaban wata hukuma kawai ina zaune sa iyane zanyi aure na haihu ina ilimin addini na dai dai gwargwado ina bautawa Allah ina kare iyakokin dokokin ubangiji na, kawai wani yazo yaci zarafina in kyale shi.
Saboda ina tsoron abinda mutane zasu ce nabari abu ya tafi haka kawai saboda Allah nake bautawa na yarda shine Ubangiji annabi Muhammadu (s.a.w)shine abinda nafi kauna a rayuwata, ina son iyayena inason iyalina, ina son dangina da abokaina wani yazo yaci mutunci na in kyale shi.
Na dauki wannan hukunci ne domin yazo ya lissafo sunayen wadannan mutane da suke aikata abun da ya fadi, na bashi awa arba’in da takwas 48 kamar yadda lauyana ya rubuta.
Ko yazo ya cire ni daga wannan maganar da yayi da duka mutane ko kuma akasarin masana’atar da suke aikatawa na rashin daidai bana daga cikin wadannan idan kuma bai zo ya kare kansa ba zamu tafi kotu, kuma ina fatan kotu zata ji korafi na zatayi adalci wannan shine dalilina na rubutu masa wannan takarda kuma shine dalili na zuwa kotu nan gaba- inji Alhaji sheshe.