Ƴansanda sun ƙaryata labarin ‘kwashe balance’ a Borno


Yansanda a jihar Borno a jiya Talata sun ƙaryata labarin ɓacewar mazakuta a Maiduguri.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a yan kwanakin nan an sake dawo da batun satar mazakuta, inda na wannan karon ya zo da sabon salo, wanda masu amfani da kafofin sadarwa na yanar gizo su ka yi masa lakabi da ‘satar balance.
Kakakin rundunar ƴansanda a jihar, ASP Nahum Daso, ya bayyana ikirarin da wasu su ka yi cewa an sace musu mazakuta ƙarya ne, kuma labari ne maras tushe.
Daso ya bayyana cewa ƴansanda sun samu bayanan ƙarya da wasu mutane ke yadawa kan bacewar al’aurarsu, yawanci bayan sun yi musabaha da baki.
Ya kara da cewa wadanda abin ya shafa da suka kai kara an kai su asibiti domin duba lafiyarsu sai dai an gano cewa zargin ba shi da tushe balle makama domin al’aurarsu na nan daram kuma tana aiki.
“Dangane da wannan batun, ƴansanda na son sanar da mutanen Borno kada su firgita; su kasance masu bin doka da oda tare da yin watsi da labaran ƙarya da ka iya haifar da rashin jituwa da rushe yanayin zaman lafiya a jihar.
“Yansanda sun kuma yi kira ga mazauna jihar da su bi doka da oda ba tare da rigima ba kuma su kai rahoton duk wani abin zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa,” Daso ya kara da cewa.