AddiniLabarai

Zauren malamai najeriya yayi Allah wadai da ta’addancin Isra’ila akan Falasɗinawa

Prof. Mansur Ibrahim Sokoto shine ya fitar da wannan sanarwa a shafinsa na sada zumunta na facebook.

Zauren Malamai a Najeriya ya bi sahun miliyoyin al’ummar musulmi da sauran mutane ma su tausayi wajen yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin yahudawan Isra’ila ke yi wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba a kasar Falasdinu. Wadannan hare-haren dai suna zuwa ne a wani bangare na ci gaba da kwace da mamaye yankunan Falastinawa da sojojin yahudawa suke yi tun bayan kafa haramtacciyar kasar Isra’ila fiye da shekaru saba’in da suka gabata, a dai dai lokacin da kungiyoyin kasashen duniya su ka nade hannu ku ma su ka zuba ido game da haramtattun matakan da Isra’ilawa ke ci gaba da dauka na hallaka da raunata yara da manya, maza da mata, baya da kuma cin zarafin wadannan bayin Allah, wadanda da ba su ji ba ba su gani ba.
Zauren Malamai ya na kira ga Majalisar Dinkin Duniya (UN) da Kungiyar Kasashen Musulumi (OIC) da Cibiyar Hadin Kan Musulunci ta Duniya (MWL) da duk sauran cibiyoyi da hukumomi da abin ya shafa cewa lalle su hada karfi da karfe, su kawo karshen wannan shiri na dabbanci da rashin imani da Isra’ila ta yi kaurin suna wajen aiwatarwa a kan kan fararen hular da ba su da ikon kare kan su. Abubuwan da ke ci gaba da faruwa a Gaza da kuma dukkanin yankunan Falasdinawa da aka mamaye, yana ci gaba da yin izgili ga dukkanin kungiyoyin kasashen duniya, musamman ma cibiyoyin duniya masu karfi da ake cewa an kafa su don tabbatar da ‘yancin kai da kare hakkin ɗan adam da ‘yancin rayuwa.

Babban abin kunya ne ga Majalisar Dinkin Duniya ta kasa samar da mafita ta dindindin a rikicin Falasdinu, kuma ta ci gaba da barin Isra’ila ta na yi karan tsaye ga dukkan kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, bayan kwashe shekaru na alkawuran banza da yarjejeniyoyin zaman lafiya da suka ƙare a shirme. Haka kawai, ba tare da wani dalili ba, an maida Isra’ila kamar ta fi sauran kasashen duniya daraja, don haka ba a taba sanya mata takunkumi ba saboda wuce gona da iri ko bijirewa kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.Zauren malamai najeriya yayi Allah wadai da ta'addancin Isra'ila akan Falasɗinawa
Tabbas, al’amarin kasar Falasdinu ya fallasa munafuncin da manyan kasashen duniya ke da shi wajen sasanta sabani da warware rikice-rikice: A lokacin da su ka yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, suna masu bayyana kansu a matsayin zakarun tallafawa ‘yancin dan Adam, amma kuma a lokaci guda sun amince da kuma ba da ikon cin zarafin da Isra’ila ke yi wa fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a Gabas ta Tsakiya. Mutane da dama sun daina gaskata maganganu da kudurorin Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma galibi suna ɗaukar yarjejeniyoyinta a matsayin soki-burutsu, domin ba su da wani tasiri sai dai kawai lokacin da suke hidima ga bukatun tsirarun ‘yan tamore, ko kuma tallafawa kudurorin mulkin mallaka ta bayan gida da kuma manufofin ƙasashe masu ƙarfi waɗanda suka himmatu wajen ƙaddamar da wani sabon tsarin tafiyar da lamuran duniya bisa son zuciya.

Ya zama dole kasashen Larabawa da na Gabas ta Tsakiya su farka daga barcin da suke yi, su yi aiki tukuru don dakile zaluncin da yahudawan suke yi wa Falasdinawa. Lalle ne su gane cewa duk wani yunkurin kusantar juna da bude kofa ga Isra’ila, tamkar kwarewa al’ummar Falasdinawa baya ya ke, domin Isra’ila ba ta da wata niyya ko aniyar zaman lafiya da adalci tare da Falasdinawa.

Kuma ko da a ce kasashen Larabawa ba za su yi wannan muhimmin aiki don tausayi da son gaskiya tare da bin halattacciyar hanyar tabbatar da adalci ba, to ya kamata su yi hakan domin hana Isra’ila cimma dogon shiri da kuma burinta, da tabbatar da mugun mafarkin da ta ke da shi na samar da “Isra’ila Babba” da za ta mamaye akasarin yankunan Larabawa. da kasashen Gabas ta Tsakiya, ciki har da Masallatan Harami guda biyu. Sanarwar da Benjamin Netanyahu ya yi a baya-bayan nan game da “sabon yankin Gabas ta Tsakiya”, daya ne daga cikin matakan farko a cikin wannan al’amari, kuma idan aka bari ba tare da kalubalantar hakan ba, akwai tarin ayyukan barna da cin zarafin dan Adam da Isra’ila ta za ci gaba da yi a shekaru masu zuwa.

Don haka wajibi ne kasashen Musulmi su yi amfani da duk wata hanya da suke da ita wajen shiga cikin wannan lamari, kan-jiki-kan-karfi; ba ma kawai ta hanyar kakaba takunkumin tattalin arziki a kan Isra’ila da kawayenta wanda ke karfafa mata gwiwa a cikin mummunan aikinta a Falasdinu ba; har kuma da yin fito-na-fito da ‘kungiyoyin kasashen duniya’ game da yadda su ke yin gum, tare da nuna son kai wajen rashin tilastawa Isra’ila ta dawo kan doron doka da oda. Haka kuma lalle ne su su hada kai don tallafawa wadanda hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Falasdinu ya shafa.

Sauran Musulmi kuma, a daidaiku da kuma kungiyoyi da al’ummominsu lalle ne su rika samun damuwa da tashin hankali game da wannan musiba da mutanen Falasdinu ke ciki. Annabi (SAW) ya ce; “Muminai a fagen tausayinsu da son junansu da tausasawa a tsakaninsu kamar jiki daya ne; Idan wani sashinsa yana fama da ciwo, sauran jiki na taya shi jimami ta hanyar rashin barci da zazzabi.” (Sahihul Bukhari, 6011)
A daidai wannan lokaci ne Zauren Malamai ke kara yabawa Kasashen Saudiyya, Turkiyya, Jordan, Kuwait da sauran kasashen duniya a kan fitar da sanarwar kakkausan jawabin matsayarsu da suka yi, tare da yin Allah wadai da matakan da Isra’ila ta dauka, da kuma gargadinta cewa ta shirya daukar alhakin duk wani sakamako da zai biyo baya na wuce gona da iri na tashin hankali.

A karshe kuma, Zauren Malamai na kira ga al’ummar musulmi da ma sauran masu son zaman lafiya a fadin duniya, da su hada karfi da karfe wajen yin Allah wadai da tsokana da zaluncin da Yahudawa ke yi wa al’ummar Falasdinawa da ke rayuwa karkashin zaluncin Isra’ila, tare da yin addu’a da aiki tukuru domin tabbatar da adalci da zaman lafiya da ci gaba a duniya.

An sa hannu a wannnan jawabi ranar Talata 25th R. Awwal 1445 AH (October 10, 2023)

Aminu Inuwa Muhammad MSW, MFCE
Shugaban Zama

Engr. Basheer Adamu Aliyu
Sakatare

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button