Labarai

Za’ayi Binciki Yadda Aka Karkatar Da Tallafin Korona Naira Biliyan 183.9

Majalisar wakilai ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda aka karkatar da naira biliyan 183.9 kudaden tallafin Korona tun daga 2020 zuwa 2022 kamar yadda majiyarmu ta samu ta majiyar jaridar Leadership hausa

Kwamitin majalisar mai kula da asusun gwamnati zai binciki yadda aka kashe kudaden da aka rarraba wa ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya a matsayin tallafin Korona a wancen lokaci tare da bayar da rahoto a cikin wasu makonni domin majalisar ta dauki matakin da ya dace.

Za'ayi Binciki Yadda Aka Karkatar Da Tallafin Korona Naira Biliyan 183.9
Za’ayi Binciki Yadda Aka Karkatar Da Tallafin Korona Naira Biliyan 183.9

Binciken ya biyo bayan amincewa da kudirin da Hon. Nyampa Dauda Zakari daga Jihar Adamawa a zauren majalisa ranar Talata.

Yayin gabatar da kudirin, dan majalisar ya tunatar da cewa an ware naira biliyan 83.9 domin bayar da tallafin Korona a cikin kasafin kudi na 2020 da wata naira biliyan 100, ga kuma kudaden da hukumomin bayar da agaji na duniya suka bayar.

Ya nuna damuwarsa matuka game da rahoton bayanan kudaden tallafin Korona ta yadda aka karkatar da su daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Zakari ya damu matuka kan rashin binciken yadda aka kashe kudaden tallafin da gwamnatin tarayya da masu bayar da agaji na kasa da kasa suka ta hanyar da ba ta dace ba wanda hakan ya haifar da koma bayan tattalin arziki da tauye dama ga ‘yan Nijeriya.

Ya tunatar da cewa lokacin da Korona ta barke a 2019 ta yi matukar shafar magi-danta tare da daidaita harkokin kasuwanci da kuma tattalin arzikin kasashen duni-ya.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button