Kannywood

Wasu masu sukar gasar wakar Ƙidaya ta Rarara, Dusa ce ko Katako a Kan su – Aisha Humaira

Jaruma a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, kuma abokiyar aikin mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara, wato Aisha Humaira, tayi kaca-kaca da wasu jaruman TikTok da suka soki gasar Waƙar Ƙidaya da Rarara ya rera, inda tace akwai wadanda Dusa ce ko Katako a Kan su, akwai kuma wadanda za’a yiwa uzuri domin basu fahimci abinda ake nufi da Ƙidaya ba.

Majiyarmu ta Nasara Radio na ruwaito. Aisha Humaira wacce tayi martanin cikin wani fefen bidiyo, ta ce babu wanda aka yiwa dole akan gasar, kawai dai sun saka gasar ne domin kyautatawa ma’abota shafukan sada zumunta na zamani, domin su samu wani abu, amma kuma sai gashi anzo ana sukar abin, wanda dama halayyar yan Arewa ne, su soki duk wani abu mai kyau da dan uwansu ya fito dashi, a cewar ta.

Wasu masu sukar gasar wakar Ƙidaya ta Rarara, Dusa ce ko Katako a Kan su - Aisha Humaira
Wasu masu sukar gasar wakar Ƙidaya ta Rarara, Dusa ce ko Katako a Kan su – Aisha Humaira

“Rarara ba zai iya kawo karshen matsalar tsaro a Arewa ba, masu ganin kamar bai damu da matsalar tsaro ba, karku manta dan jihar Katsina ne, kullum cikin fargaba yake domin mahaifiyarsa da yan uwansa na can, kuma a baya yayi Waka akan matsalar tsaro, sannan kuma shi bai damu da zagin da kuke masa ba, mai ra’ayin shiga gasa ya shiga, mara ra’ayi kar ya shiga.”

Tunda fari dai wasu ma’abota shafukan sada zumunta ne suka soki batun gasar Waƙar Ƙidaya ta Rarara, bisa hujjar cewa bai yi Waƙar janyo hankalin mahukunta akan sha’anin tsaro ba, kuma bai shiga cikin kiraye-kirayen da aka yi akan kawo karshen matsalar tsaro musamman a Arewacin Nigeria ba.

Mutane sunyi martani akan wannan magana.

 

@Abdul s adam danfari abinda yake cewa:

Wato wadannan kawayen shedan din sungama Raina mutane wlh, gaskiya mutanen Kano suna sakaci dayawa.

@saleem tijjani adhama cewa yake :

Masu Dusa aka
Bazasu wuce wadanda
Suka kasa ciyar da yarsu har seda ta Gudo kano zuwa yawan ta zubar
Tareda da zaman kanta agidan da kaf danginsu babu me irin wannan Gidan .
To wannan iyayen sune masu dusa akai.

@Nura Ytilde cewa yake:

Masu Dusar Akansu suna can a MAIDUGURI domin tsabar dusar tayi musu yawa a kayi ne yasa suka barki kika zo Yawon Bariki Kano.

@Ramadan sunusi salisu cewa yake :

Kokuma tsantsar bujirewa allahce tasa kikabar gaban magabata kikuma zaman Kai da cinya.

@Buhari Yakubu yana cewa:

To wai itama katako ne akanta azo Ana sace mutane Ana kashe mutane ace ansaka wata gasar kidaya sai kifadamana menene amfanin kidaya Ana kashe mutane Wanda akashe ne za a kirga kokuma ragowar da ba a kashe ba mutane suna fama da rayuwa Dan hancin uwarki kifito kina cewa mutane basuga ne ba yanzu kowa a waye yake kowa yasan meya keyi kowa Mai hankali ne.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button