Labarai

Wani Dattijo mai shekara 71, ya killace kansa shekara 55 saboda tsoron mata

Advertisment

Labarin wani mutum mai suna Callitxe Nzamwita ya gina wata katanga kewaye da gidanaa don kada magana ko wani abu ya hada shi da mata.

Fitaccen mai amfani da manhajar sada zumunta ta titkok Abubakar sadauki wanda ankafi sani da abis fulani shine ya kawo mana wannan labari a cikin faifan bidiyo ga yadda bayyanin wannan dattijo mai karfin hali ya kasance.

” Wannan mutum da kuke gani dan shekara 71 ya kulle kansa saboda kada ya hadu da mata domin yana tsoronsu, wannan mutumin tun yana dan shekara 16-17 ya kulle kansa a wannan gida saboda bayason yaga mata domin irin tsoron su da yake yi.

Wani Dattijo mai shekara 71,  ya killace kansa shekara 55 saboda tsoron  mata
Wani Dattijo mai shekara 71, ya killace kansa shekara 55 saboda tsoron mata

Mutumin ya shafe shekara 55 bai fita daga kofar gida ba, abinda duk masu karatu zasu fara tunani shin wannan mutum ina yake samun abinci, ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa.

Advertisment

Tun daga cikin da ya kulle kansa a wannan halin yan uwansa suke kai masa abinci da ruwa da sauran abubuwa Chi da sha wasu yan uwansa da sunka fara kawo masa abinci rai yayi halinsa .

Kwatsam sai ya samu makwata a gidan nasa inda ya samu wata ƴar makwabcinsu tana taimaka masa da sauran abubuwa ,amma ita ma wannan yarinya zata kwankwasa masa idan ta aje masa ko me ta kawo masa bazai fito ba, idan yaji ta tafi sai ya fito ya dauki abun.

Abis ya fara da cewa a cikin idan yake nan ne komai nasa yake bandaki inda yake sauran lalurar da ake yi a banda daki, ya samu zantawa da likitoci ake tambayarsa miyasa yake tsoron mata, amma ya gagara baiwa likitocin amsa.

A nan ne likitoci sunka fadi sunan cutar da ke damunsa , sunanta “Gynophobia” ita wannan cutar tana samun mutum idan wani babban al’amari na tsoro ya sami mutum akan mace- inji abis fulani

Ga bidiyon nan ku kala domin ganin wnanan mutumin da yake tsoron mata da inda yake rayuwa.

@abis_fulani Shekararsa 56years a kulle sabode yana tsoron haduwa da mata #abis_fulani #hausa #nigeria #kano ♬ original sound – Abubakar sadauki????????

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button