Tsadar rayuwa ta sa wata mata sayar da jikanta kan kudi Naira dubu 50 a Nijeriya
Wata mata mai suna Mrs Oluchukwu Nwosu ta sayar da jikanta dan watanni uku kan kudi Naira dubu 50, inda ta zargi halin matsin rayuwa da cire tallafin man fetur ya ingiza ta a Nnewi ta jihar Anambra.
Mrs Nwosu ta ce diyarta da ta haifi wannan jariri, dama ta taba haihuwar wasu biyu a baya, ta sakar mata, tana ta wahala da su, inda ta ce ba ta da karfi, yanzu haka wadancan yaran biyu na gidan marayu na Awka, jaridar Dclhausa na ruwaito
Matar na neman yafiya, sai dai ta ce tana cikin halin matsin rayuwa tun bayan da diyarta ta haihu, ba su iya cin abinci sau uku a rana.
Tochukwu Asiegbu ne dai ake zargin ya sayi wannan jariri sabuwar haihuwa. Sai dai kwamishinar mata ta jihar Anambra Lfy Obinabo ta tabbatar da cewa an ceto jinjirin da aka cefanar.
Wani labari na daban: Shugaba Tinubu ya sanar da lokacin da za a fara ba daliban Nijeriya bashin kudin makaranta
Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar da a watan Janairun 2024 za a fara ba daliban kasar bashin kudin da za su dauki dawainiyar karatunsu.
Shugaban kasar da ya furta haka a a Abuja wajen taron kula da tattalin arziki, ya ce idan aka aiwatar da hakan, batun yajin aikin malaman jami’o’i zai zamo tarihi.
Shugaban kasar ya kuma yi magana sosai kan yadda gwamnatinsa ta yi tsare-tsare don ganin an saita tattalin arzikin kasar.