Labarai

Tinubu na kitsa yadda zai yi shekaru 8 amma ba za mu yarda ba – Sheikh Ahmad Gummi

Malamin addinin Islama Sheikh Abubakar Gumi ya ce Shugaba Tinubu da mutanensa na kitsa yadda za su yi shekaru takwas a kan mulkin Nijeriya amma a cewar malamin shugaban ba zai samu biyan bukata ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito malamin a wani faifan bidiyo na fadin yadda gwamnatin Tinubu ta mayar da arewacin kasar saniyar ware. Ya ce an nada ministocin tsaro Musulmai amma a zahiri manyan sojoji da ke bayar da umurni a fagen daga ba Musulmai ba ne.

Tinubu na kitsa yadda zai yi shekaru 8 amma ba za mu yarda ba - Sheikh Ahmad Gummi
Tinubu na kitsa yadda zai yi shekaru 8 amma ba za mu yarda ba – Sheikh Ahmad Gummi

A cikin bidiyon kuma malamin ya nuna rashin jin dadinsa da kamun ludayin ministan Abuja Nyesom Wike, wanda malamin ya yi zargin na gab da mayar da Abuja matattarar Yahudawa tamkar birnin Tel Aviv.

Wani labarin na daban : Kotun koli ta sanya ranar da za ta saurari karar Atiku kan nasarar zaben Tinubu

Kotun kolin Nijeriya ta ce a ranar 23/10/2023 za ta saurari bukatar da madugun adawa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya gabatar mata domin duba yadda za ta soke nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Hukumar zabe ta INEC dai ta ayyana Shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023. Kotun sauraran kararrakin zabe ma ta tabbatar da wannan nasara ta Tinubu.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button