Labarai

Tiktoker: Daga Ƙarshe Rahama Sa’idu da anka kora daga makaranta tayi magana

Advertisment

Wata daliba a kwalejin ‘ nursing and science birnin kebbi’ da anka kora daga makaranta sakamakon wasu na cewa irin yadda take abubuwa a kafar sada zumunta ta tiktok abun yayi yawa.

Kwalejin Koyar da aikin jinya da kimiyya KBCONS Dake jihar Kebbi a Arewacin Najeriya ta kori fitacciyar ‘yar tiktok Rahama Saidu daga karatu a makarantar, sai dai wasu na ganin cewa sakamakon badala da ta ke yi a kafar tiktok ne ya jawo mata dakatarwar

Tiktoker: Daga Ƙarshe Rahama Sa'idu  da anka kora daga makaranta tayi magana
Tiktoker: Daga Ƙarshe Rahama Sa’idu da anka kora daga makaranta tayi magana

Sai dai kuma hukumar makarantar College Of Nursing and Science Dake Jahar Kebbi ta kori wannan zargin in da take cewa ta kori dalibar ne sakamakon kin bin umarni da kuma dokokin makranta ciki har da kin zuwa Makaranta kusan na sati uku, kuma dalibar tayi Rashin nasara a jarrabawa guda biyar.

To shine ta fito tayi wani bidiyo inda take bayyanin cikin alhini tana kuka akan yadda rayuwar ta zata shiga cikin garari ga abinda take cewa :

“An kori ni a makaranta ba jindadi na bane nice babba a gida mu, mu bama su karfi bane wato rufin asiri ne ba yar masu hannu da shuni bace ina da ƙane shidda ga iyayena ban san ta inda zan fara ba, da sun ce in daina kasuwanci bazan iya daina kasuwanci ba, saboda da kasuwanci nake rufawa kaina asiri da taimakon ƙanena.

Rahama saidu ta kara da cewa idan anka hanani kasuwanci na ba’a yimin adalci ba- inji rahama saidu.

Hausaloaded tayi korari wajen tattaro mutane da sunkayi sharhi akan karkashin bidiyon.

@saboalabbas cewa yake :

Na tayaki bakin ciki rahama daman kina makaranta shine kike irin wannan sam bai kamaceki ba social media babu abinda zai baki a rayuwa maimakon kiyi ki kulaakan buri dinki ki taimaki kanki da qanninki amma yanzu kinga abinda ya faru Allah ya baki mafita kuma kiyi hakuri ki daukeshi a matsayin kaddara.

@sadatadamkaria cewa take :

Yi hakuri rahma but wannan issue ba wanda Zaki fada a anan bane kawai kiyi addu’a and kici gaba da kasuwanci dinki na baki shawara kamar yadda nace a farko kiyi hakuri.

@blacksliter cewa yake :

Yaushe makaranta ya koma hana kasuwanci kuma????!!! Wannan kam da sake.

@yusufmusa2936 cew yake:

Aslm .abubuwa da mu tan nigeria mukeyi bama kyautawa kuma shuwa gabannin mu muji tsoron Allah , kaddara mah wani abu takeyi wanda baidace bah wa’azi yakama ayimata da hikima domin tagyara , in ance antimata haka to ba anemi tashiryuba anyine a tarwatsa mata rayuwa wallahi , domin hakan data shiga ta iya yuwuwa tafada wata dabi’ar data fi wancan , kaga mai.makon gyara ankara bada gudun mawar rayuwar ta takara lalacewa mai makon ataimaketa tagyara domin tadawo kan hanya madaidai ciya , saboda ga shawara indai wannan shine mafita to wallahi wannan ba shine mafita ba anyine akara tarwatsa mata rayiwa bawai agyara mata rayuwa bah, yah allah kashiryar damu kayi dukkan nin musulmai tsari daga wani abu mai cutarwa ko zullimi ameen.hattara yakai Dan adam kukan kurciya mai hankaline ke ganewa.

@beeanchau cewa yake:

Kinsan da duk wannan abubuwa Amman baki daukan shawaran mutane rayuwar wake wake bazai amfana miki komai bah, Ubangiji Allah yakawo miki mafita.

@abdul’ib cewa yake:

Hmmm duk kinsan da wannan kikeyin wannan a social media kk tona wa kanki asiri dai yanzu ke Mutum dan mutunci da kima zai aureki ne kowa a social media ya san abunda kke yi na watse wa Allah ya shiryeki

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button