Labarai

Talauci: Yunwa ta yi sanadiyar ajalin wani magidanci yabar mata da ciki,ga ƴaƴa ba abinci

Advertisment

Mun binciki labarin wata baiwar Allah a jihar Kano mai suna Binta wacce yunwa ta kashe mijinta, Sani mai Faskare, yanzu haka ita da ‘yayanta Biyar suna cikin mawuyacin hali, ba abinci, ba makaranta, ba lafiya, Baba ya mutu, mama nada ciki gashi tana idda bata iya fita, yunwa na neman halaka su, kwatsam sai gashi kuma an bata “notis” ta tashi daga kangon da take maneji ita da ƴaƴanta Biyar su tashi nan da ƙarshen watan nan, Majiyar ta samu ta majiyar wakiliya na ruwaito.

Talauci: Yunwa ta yi sanadiyar ajalin wani magidanci yabar mata da ciki,ga ƴaƴa ba abinci
Muhallin da wannan baiwar Allah da iyalinta suke rayuwa

Ma’aikaciyar Wakiliya, Jidda Adam ta yi tattaki har wajen da matar take inda ta tattauna da ita sannan ta dauko bidiyon mawuyacin halin da Binta da ƴaƴanta suke ciki.

Yau watansa guda da rasuwa,

Talauci: Yunwa ta yi sanadiyar ajalin wani magidanci yabar mata da ciki,ga ƴaƴa ba abinci
Inda suke rayuwa abun akwai ban tausai sosai

Jidda ta gano cewa Binta, ta kasance tana yin sana’ar wankau da surfe domin rufawa kanta asiri a yayinda mijinta margayi Sani ke yin sana’ar faskare,

Ƴaƴanta suna zagaye da ita, a cikin kuka mai sosa zuciya Binta yar kimanin shekara 40 ta bamu labarin cewa “Sakamakon tsadar rayuwa ba ta samun wankau shima margayi baya samun aikin faskare sosai tun muna kacan-canawa yaranmu dan abunda muka samo idan mun fita ni da shi, har takai ga rashin lafiyar yunwa ya kwantar dashi, jikinsa yayi tsananin ya roƙe ni inje in roƙo ko Naira 200 ce in sayo masa abinci yaci ya sha magani ganin cewa ƙirjinsa nayi masa ciwo sosai a lokacin, Na fita domin inyi fafutukar nemo kudin amma ko kafin in dawo sai dai na zo na tarar da gawarsa, ya mutu”

Wakiliya ta ruwaito matar wacce a yanzu haka take da ciki, sai ta tura yaranta su je suyi bara kafin suke samun na abincin ci, saboda tana idda yanzu ba hali ta fita ko ina, balle ta yi surfe ko wankau da take yi, a cikin kuka Binta ta ce “watarana basa samun ko abincin ci idan yaranta sun dame ta suna jin yunwa sai dai ta tasa su suyita kuka”

Talauci: Yunwa ta yi sanadiyar ajalin wani magidanci yabar mata da ciki,ga ƴaƴa ba abinci
Allahu Akbar akwai ban tausai wallahi

Mahukunta da jama’a wannan ƙalubale ne garemu baki daya, mu dai munyi namu sauran naku, Binta tana zaune ne a karamar hukumar Gezawa dake jihar Kano a wata unguwa da ake kira Unguwar Rummawa, Arewa da Sauna ana iya tuntubar Jidda Adam wacce tayi dawainiyar zaƙulo mana wannan rahoto a wannan lambar 0809075124089 domin gani da ido da taimakawa wannan baiwar Allah

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button