Shiririta da rawar kai tasa bazan iya aure ko soyayya da ɗa kasa da shekaru 30 ba – inji budurwa fareedah tofa
Shirme Da Wautar Samari Ƴan Ƙasa Da Shekaru 30 Yasa Nace Ni Bazan Iya Aure Kó Soyayya Da Irin Su Ba
Farida tofa ta samu zantawa da Dokin karfe tv inda ankayi mata tambayoyi da dama harda takaitaccen tarihin rayuwarta, Fareedah Tofa wanda ake yiwa lakabi da minista, tace mukamin minista yana cikin babban burinta ta zama wannan kujerar.
Fareedah tofa tana daya daga cikin masu amfani da kafar sada zumunta a facebook wanda tana daya daga cikin masu jawo CeCe kuce a kafar sada zumunta a manhajar facebook.
“Ni bana son shiririta nafison mutum babba wanda zaiyi min magana da za’a ci gaba a rayuwa, yaro yana da rawar kai yana saboda ko ni da nake mace banson rawar kai balanta ga yaro .
Idan kina soyayya da yaro zaki dinga ganin matsaloli babba kuwa kina ganin yana girmama kanshi kima kina girmama kanki Idan keyi kuskure zai gyara miki ya fahimtar da ke wannan shine dalilin da yasa bana shiga sabgar yara gaskiya “- inji Fareedah
Sannan ta bawa mata shawara cewar duk namijiń da yazó gurin ki tambaye kai tsaye , My dear ki cire tsoro “Aurena kake sonyi” idan ya ce dake “eh” kice ya turo. Idan kuma ya faɗi akasin haka Malama ki sallame shi, ko da kuwa kina mishi som duniya domin ba masoyinki bane.
Ga bidiyon nan.