Kannywood

Shan Maganin Karfin Maza Ya Maida Magidanci Abin Kallo A Gari

An garzaya da wani magidanci asibiti, bayan da ya sha maganin karfin maza, gabansa ya ki kwantawa duk da kokarin ’yan uwa da abokan arziki na shawo kan al’amarin.

Wani kwararren ma’aikacin jinya a Asibitin Kwararru na Sakkwato, Ibrahim Abdullahi, ya ce, saura kiris a yanke shawarar yi wa mutumin tiyata a gabansa, domin sai da suka shafe kwana uku suna jinyar mutumin kafin gaban nasa ya kwanta jaridar Aminiya Hausa na ruwaito.

Ibrahim wanda ya ce mutumin ya zama abin kallo har ga kawayen matansa, ya bayyana cewa “Da ba mu samu nasara ba, za a yi masa aiki ne ta kwanta amma ba za ta sake tashi ba har abada.”

Yaya za ka ji idan da kai ne wannan mutumin, ko a ce mijinki ne hakan ta faru da shi?

Shin me ke sa mutane shan maganin karfin maza

Yaduwar shan maganin karfin maza
Maganin karfin maza ko maganin kara kuzarin namiji da sauran sunayen da ake kiran su a cikin al’ummar Hausawa, sha da amfani da shi ya zama ruwan dare a wannan yanki na Arewa.

Maganin yana cikin kasuwancin da mutane da dama suke yi wanda kuma ake samun kudi a cikinsa a wannan zamani.

“Wannan lokaci amfani da maganin maza ya yi yawa; Abu biyu nake ganin ya haifar da amfani da maganin, mata da yanayin abincin da muke ci a yanzu.

“Mata a bangarensu suna fifita maganar batsa sama da komai.

“A duk sa’ar da suka hadu a gidajen biki sukan tayar da hirar kwanciya tsakaninsu da mazansu, a nan ne wata za ta ji mu’amala daban da yadda mijinta yake yi mata, sai ta kudirta sai mijinta ya kwanta da ita kamar haka.

“Wata da kanta za ta fada masa ya sha magani don ya yi mata yadda za ta gamsu.

In kuma tana tsoronsa a cikin matan da suka ba ta labari za ta nemi su samo mata maganin ta sanya wa mijin a abinci ya ci ba tare da ya sani ba, a hakan za ta bi da shi har ya ci gaba da mu’amala da maganin domin kokarin samun gamsuwarta”, in ji Muhammad Inuwa, manazarci kan al’amuran yau da kullum.

Ya ci gaba da cewa, “A gefen abinci kuma da yawa mutane na fadin abincin da muke ci yanzu musamman magi na daskare kuzarin namiji.

“A kokarinsa na gamsar da iyalinsa sai ya koma shan maganin maza, da wuya hukuma ta yi wani abu a kai don ko maganin kiwon lafiya ba a kula da shi yadda ya dace ballantana na maza da ake kallon wani abu ne na ganin dama kawai.

“In da matsalar take har yau ban ji masana sun fadi illar maganin nan karara ba sai dai kame-kame domin ba wani magani da ba ya da illa, tun daga farasitamol, ko an ce maganin maza na da illa, sai mu ce wace iri, don ni mutum daya ne na ji cewa ya makance kan amfani da maganin maza a Jihar Katsina.

“Bayan shi ba wani bayani sai dai ka ji ana cewa suna haifar da ciwon hawan jini ko na hanta ko ciyon rashin tsayawar fitsari.

“Amma a zahiri ka ga illar a wurin mutum dattijo ko matashi babu,” in ji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button