Labarai

Satar mutane yanzu muka fara – in ji dan bindiga Dogo Giɗe

Babban dan bindiga nan da ke zaune a yankin jihar Neja gefen kontagora ya fitar da wani sabon sako zuwa ga al’umma najeriya wanda yana so wannan sako ya yaɗa shi ya tafi ko ina a cikin wani faifan sautin murya da yake a shafukan sada zumunta inda Bello muazu ya dora a shafinsa.

Idan baku manta kwanan baya anga bidiyo da ya fitar wanda yaransa suke ikirarin sune sunka tarwatsa jirgin sojoji da yayi sanadiyyar mutuwar hazikin sojojin Najeriya.

Satar mutane yanzu muka fara - in ji dan bindiga Dogo Giɗe
Satar mutane yanzu muka fara – in ji dan bindiga Dogo Giɗe

Ga abinda yake cewa :

Satar mutane yanzu ma munka fara saboda akwai dalili saboda satan da ankayi yanzu ne ma zamuyi shi, kuma ina son wannan sako ya ishe kunnen kowa dan Allah.

Yanzu tsakanina da Allah yanzu in kaji nayo sata mutum goma na rantse da Allah a gabar da wannan labarin mutum bakwai 7 zan kashe mutum ukku zasu koma, inaso in gayawa duniya su karya sukeyi ni banma son sulhun wallahi bani son sulhu bana ni wallahi banima son zama lafiya.

Dogo giɗe ya kara da cewa:

“Ni wallahi duk mai neman zama lafiya baida albarka ni na yarda zamana lafiya naci na sha da iyalina cikin daji, in sha Allahu nidai da gari sai dai in bayan rayuwata na hakura da gari.

Ni daji yanzu ya zamu uwata ya zamu ubana cikin daji nan ne zan ga wuya in boye in samu daɗi na inyi zama na, ina rokon Allah ya tayani zamana a cikin dajin nan.

Bani buƙata gari ko miliyan dubu gwamnati zata bani dan in daina ta’addanci wallahi na yafe, ranar ta same ni bana son ta barni da rayuwata.”- inji dan bindiga.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button