Rana dubu ta ɓarawo :Sojoji sun yi nasarar aikawa da wani ƙasurgumin ɓarawo ɓarhazu, da ya addabi ƴan arewa
Jami’an tsaron Najeriya sun kashe wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a yankin arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda wani jami’i ya bayyana.
Ahmed Idris, mai magana da yawun gwamnan Kebbi, Nasir Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.
kamar yadda Majiyarmu ta Premium Times Hausa na ruwaito,ya ce an kashe ɗan bindigan mai laƙabin Mai-Nasara ne a wani samame da jami’an tsaro suka kai a dajin Sangeko a jihar Kebbi. An kuma kama wasu mutane biyar da ake zargin yaran Mai-Nasara ne a yayin wannan farmakin.
Yayin da yake yaba da irin namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi na yaki da miyagun laifuka a jihar, musamman a kudancin Kebbi, AbdulRahman Usman, babban Darektan tsaro a ofishin gwamna ya yi kira ga jama’a da su rika ba jami’an goyon baya da hadin kai domin samun nasara.
“Taimakon ku da hadin kan ku ya zama wajibi matuka ga jami’an tsaro don cimma burin da ake so na fatattakar masu aikata laifuka da kuma dawo da zaman lafiya ba a jihar ba kawai, har da kasa baki ɗaya.
Jami’an tsaro sun kara kaimi matuka wajen kai farmaki ga ƴan bindiga musamman a jihohin Arewa maso yamma da wasu jihohin kasar nan.
A Wani labarin: An maka tsohon kwamishinan Ganduje kotu da ya haramta auren zawarawan da aka yi kwanan nan a Kano
Wasu Angwaye da Amaren auren Hisbah sun yi ƙarar tsohon kwamishinan Ganduje Malam Garba Yusuf a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta Kasuwa da ke Shahuci karƙashin Mai Shari’a Abdu Abdullahi Wayya.
Angwaye da Amaren na zarginsa da sheganta musu aure.
Kotun ta sanya ranar 6 ga watan Nuwamba mai kamawa domin soma sauraron shari’ar.