Labarai

Phram Isah Dahiru da ya ci gasar fasaha da kirkira ta NCC yaci kyautar Naira miliyan Goma ₦10million

Wannan da kuke gani shi ne Pharmacist Isah Dahiru da ya ci gasar fasaha ta kirkira da Nigerian Communications Commission (NCC) ta sa, wanda hakan yasa ya samu kyautar Naira Miliyan Goma.

Ya ci wannan gasan ne a sakamakon Kirkira da yayi na Abin Taimako ga masu matsalar rashin iya riƙe fitsari a sanadiyar dalilai kamar tsufa, rashin lafiya da sauransu. Sunan abin kirkirar shi “Smart Bladder”.

Wannan abun dai kamar Pampers ne da ake sawa amma yana da takanoloji na bawa mutum damar sarrafa aikin marar shi (Bladder).Phram Isah Dahiru da ya ci gasar fasaha da kirkira ta NCC yaci kyautar Naira miliyan Goma ₦10million

Wannan fasaha ce mai ban sha’awa da ta kasance ta Farko a wannan nahiyar tamu. Muna Alfahari dashi da wannan kirkira tashi.

Ga wanda basu sani ba, Isah Dahiru ɗan ajinmu ne a Jami’ar ABU Zaria kuma tare muka kammala karatu. Saboda haka wannan nasara ta dukkan yan ajinmu na U13PH ne da mutanen Arewa da Nijeriya gaba daya.Phram Isah Dahiru da ya ci gasar fasaha da kirkira ta NCC yaci kyautar Naira miliyan Goma ₦10million

Tabbas al’ummar mu akwai fahasa. Allah ya taimaka.
Jama’a ku taya shi murna domin alfahari da shi a matsayin ɗan Arewa, ɗan Nijeriya, ɗan Afrika.

Phram Isah Dahiru da ya ci gasar fasaha da kirkira ta NCC yaci kyautar Naira miliyan Goma ₦10million
Wannan itace SMART BLADDER DEVICE

MiNENE SMART BLADDER DEVICE?

 

Wata sabuwar na’urace muka kirkira domin magance matsalar yin fitsari batare da sanin mutum ba.

Mutane masu shekaru da dama, mata wadanda suka haihu akan magudanar fitsarin su, da kuma wasu masu cututtuka irin su ciwon suga, ciwon rawar gabobi da sauran cututtukan laka, za’a ga cewar fitsari nazuba ta gabansu batare da suna son hakan ba. Yara kanana ma wasu sukanyi fitsarin kwance har takai ga suna kamuwa da wasu cututtukan.

Fitar fitsari batare da son mutum ba damuwa ce ta wasu abubuwa guda uku da ake ce musu nerves (jijiyoyin kaiwa sako kwakwalwa)

Idan suka samu tangarda, ko kuma suka tsufa, ko kuma suka sarke da juna, to sako bazai na isa kwakwalwa ba akan ayi fitsari, ko kuma abari sai anjima.

Wannan dalili yasa mukayi wannan na’ura, zata dauki sakon ayi fitsari ko abari sai anjima da kanta takai wa kwakwalwa, batare da jiran wadancan jijiyoyin ba.

Kunga kenan, ita tana aiki ne ta hanyar kwaikwayon nerves din.

An samar da ita ta hanyar kirkirarriyar fasahar dan Adam (artificial intelligence) da kuma amfani da siddabarun na’ura mai kwakwalwa (computer simulation algorithms)

Zata saukakawa mutane masu matsalar yoyon fitsari, sannan kuma zata rage musu kashe kudin kula da lafiyar mafitsara da kaso 78 cikin dari.

Muna godiya ga hukumar Nigeria, da hukumar sadarwa da suka saka fasahar mu a matsayin ta daya a fadin Nigeria.

Nagode,
Pharmacist Isah Dahiru
Mai Kirkira, Shugaban Kamfanin Specxs Care Limited.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button