Addini

Mun samu masu juna biyu da ƙanjamau a cikin aure zawarawa a kano – Hisbah

Kano – Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an samu wasu da ke dauke da cututtuka a cikin wadanda ke neman ayi masu auren gata.

Vanguard ta ce cututtukan da aka samu sun hada ciwon hanta na Hepatitis B, sikila da kanjamu.

Mai magana da yawun bakin hukumar ta Hisbah, Lawan Fagge ya ce an gano wannan ne a wajen gwaje-gwajen da ake yi kafin auren

Hisbah ba za tayi aure da ciki ba
Har ila yau akwai matan da aka samu su na dauke da juna biyu a yanzu haka. A musulunci, ba a yin aure dauke da ciki har sai an yi tsarki, jaridar legit na ruwaito.

Mun samu masu juna biyu da ƙanjamau a cikin aure zawarawa a kano - Hisbah
Mun samu masu juna biyu da ƙanjamau a cikin aure zawarawa a kano – Hisbah Hoto/Facebook: Aminu Ibrahim Daurawa

Malam Lawan Fagge ya ce tuni an maye guraben irin wadannan mutane da aka samu da wasu dabam domin su ci moriyar tsarin gwamnatin.

Hukumar Hisbah za ta taimakawa masu dauke da cututtukan da maganguna, kuma ana basu shawarwarin ganin yadda za su samu lafiya.

Jawabin Kakakin Hukumar Hisbah

Idan sun samu lafiya, Fagge ya ce nan gaba za a iya aurar da masu dauke da wadannan cututtuka.
Wannan ya na cikin rahoton farko da mu ka samu daga ma’aikatar kiwon lafiya.
Akwai kusan maza da mata 40 da ke da cutar Hepatitis B. Akwai masu cutar sikila, sai kuma masu juna biyu da wadanda ke dauke da kanjamau.
Amma a wata mai zuwa za a fara ba su shawarwari kuma a ba su magunguna. Ba a karbe su cikin tsarin ba, amma an maye gurbinsu da wasu.
Za a iya la’akari da su idan sun jurewa shan magunguna kuma sun karbi shawarwarin.
– Malam Lawan Fagge

Da yake jawabi, kakakin na Hisbah ya ce sun tantance masu neman aure kusan 5000, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta aurar da mutane 1800.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button