Labarai

Mun dakatar da shirin N-power – Dr. Betta Edu

Advertisment

Ministan jinkai da wahala dr betta edu ta ayya na shirin N-power shiri ne da yake wahalda ita a koda yaushe wanda tace wannan shirin akwai rikici sosai a cikinsa ta fitar da wannan sanarwa cewa akwi yiyuwar baza’a sake biya ba sai farko na shekarar 2024.

To sai yanzu kuma ga wata sabuwa sanarwa wadda take cewa akwai matsololi da dama da wasu naci kudin shirin inda dole sai an samu mafita akan wannan alamarin.

Majiyarmu ta samu ta majiyar wani fitaccen mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook Rabiu Biyora inda ya fitar da wannan labarin cewa babu maganar N-power a halin yanzu ga abinda yake cewa:

Mun dakatar da shirin N-power - Dr. Betta Edu
Mun dakatar da shirin N-power – Dr. Betta Edu

Ministar Jinkai da Walwala Betta Edu ta sanar da dakatar da shirin N-POWER domin a gudanar da binciken yadda aka saka sunayen mutane da yadda aka dinga fitar da makudan kudade da zummar ana rabawa al’umma….

Lallai ne a wannan karon sai an bincika zare da abawa a tabbatar cewa wasu basuyi amfani da shirin ba wajen azurta kansu, sannan dole ne duk wanda aka samu hannunsa cikin almundahana yayo aman abun da ya kwasa ko ta kwasa…

Shirin zai dawo bisa aminci bayan an kammala bincike..”

Daman mutane da damu suna tunanin cewa ba dole bane wannan gwamanti ta yi tafiya da duk wani shiri da anka kirkira a lokacin Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button