Mun dakatar da sayar da littafin “Queen primer” a kano – Abba Elmustapha
Hukumar tace fina finai ta dakatar da sayar da Littafin "Queen primer"
Littafin Queen primer Littafi ne da ake karantar da yara yan nursery da primary a makarantu sai anka fahimci akwai kalamai na batsa ko fasadi a ciki akwai kalma “gay” luwadi kenan wanda ake koyar da yaran a makarantu, gidan rediyon Rahama tv ta samu tattaunawa da abba elmustapha shugaban hukumar tace fina finai da ɗabi’a a jihar Kano.
Shine hukumar tace fina finai da dabi’a a jihar kano ta dakatar da sayar da littafin Queen primer a duk fadin jihar kano kamar yadda shugaban hukumar tace fina finai da ɗabi’a, abba elmustapha yake sheda wa manema labarai.
“To alhamdulillahi kowa ya tashi ya kwana a kano mu tashi da wata annoba ta wani littafi da ake koyar da yaranmu a “primary da nursery” mai suna Queen primer wannan littafi cike yake da kalamai na fasadi wanda bai kamata ace ya’yan mu sun ji shi ba, ko an karantar da su, da wannan ina shigowa ofis a yau na bazama na tura operation team dina gaba daya su shiga duk wata kasuwa da ake sayar da duk wani littafi.
An ka samu yin rankata kaf gaba daya anka kawo su ofis zamu cigaba da bincike har zuwa gaban kuliya ga wanda munka gani yana sayar da littafin, saboda haka gwamnati ta dakar da sayar da wannan littafi ko takwarorinsa, ta hana amfani da shi a cikin garin kano baki daya, sa’a nan duk wasu makarantu da suke amfani da shi wajen karantar da ɗalibai shima mun hana kuma munyi barnning dinsa gaba daya a jihar kano.
Duk wani wanda munka kama yana sayar da shi doka zatayi aiki akansa, yanzu haka mun kama kwara dubu na littafin Queen primer kuma mutanen suna can suna bincike -inji abba elmustapha.
Ga bidiyon nan.