Labarai

Maganar gaskiya akan sace al’aurar ɗa namiji – bincike masana

Maganar shafe mulera wanda abun yanzu yake gasgatuwa a arewacin najeriya wanda wani likita masanin ilimin lafiyar dan adama pharm. Musa A. Bello ya fitar da bayyani a ilmance a shafinsa na sada zumunta ga abinda yake cewa .

Mutane da yawa basu san tunani na da alaƙa da warkewa a yayin rashin lafiya ba. Yadda mutum yasa a ran shi, yana tasiri wajen aiki. Shi yasa ko ruwa (water) ka diba ka ba wani kace mishi wani magani ne na musamman da zai taimaka mishi wajen warkewa daga wata matsala, sannan ka tabbatar mishi da wasu ma sun yi amfani da shi sun dace, toh fa in ya sha, sai yaji alamun fa hakane, maganin na aiki. Ƙarfin tunani kenan.

Hakazalika, sha’awa (Sexual Arousal) na kwanciyar aure nada alaƙa da tunanin zuciya.Shi yasa namiji ko tunanin matar shi yayi a wani yanayi, sai yaji al’aurar shi ta amsa duk da cewa baya ganin ta a lokacin.

Maganar gaskiya akan sace al'aurar ɗa namiji - bincike masana
Maganar gaskiya akan sace al’aurar ɗa namiji – bincike masana

Shi matsalar da ɗa namiji zai ji baya jin Al’aurar shi ake ce ma “KORO SYNDROME”. Matsala ce da take da alaƙa da ƙwaƙwalwa/tunani. Zai ji kamar abin na zukewa cikin jikin shi ne wanda hakan zai tada mishi hankali. A wajen mace kuma za ta ji kamar kan mamanta ko leɓen al’aurar ta na nokewa ciki.

Duniyar ilimi ta tabbatar da cewa Matsala ne na Ƙwaƙwalwa/Tunani (Psychiatry Disorder) wanda yake samo asali daga mabanbantan dalilai kamar haka:

1. Yawan Tunani akan girman al’aurar mutum.
Zan iya cewa mutanen da suke yawan mun tambaya akan yadda za su ƙara girman abin su sun fi masu tambaya akan yaya za su yi ƙiba. Hakan ya nuna mutane da yawa sun damu da tunanin ƙara girman abin wanda duniyar ilimi ta tabbatar da babu abinda zai ƙara maka girman shi In ba aiki na musamman ba (surgery). Azzakari na iya girma iya ƙarshen girman shi yayin sha’awa, amma ba zai wuce ainihin girman shi ba.

Saboda mutane sun sa ma kansu tunanin kankancewar gaba, shi yasa kullum masu maganin abin suke ciniki sosai. In ka gaya ma mutum ba wani matsala game da girman abin shi, sai ya ga kamar kana mishi baƙin cikin samun katoton abu ne, duk da girman abun bashi da alaƙa da farin cikin da zai ji ko ya bayar.

2. Yarda Da Cewa An Mishi Sihiri
Mutum na fara tunanin cewa wanda fa ya goge shi yanzun nan, ɗan shafi mulera ne, nan fa ƙwaƙwalwar shi za ta fara raya mishi cewa abin nashi fa ya bace, wanda a zahiri ba haka bane.

3. Yawan Istimna’i/Wasa da Al’aurar Mutum Shi da kanshi (Masturbation) Wannan yana haifar da wannan tunanin.

4. Tunanin Cewa Dole Azzakari Sai Ya Kai Inci Sha Biyar (15inches) kamar yadda ake faɗa a wasu littattafan soyayya na karya (novel). Wannan yaudarar kai ne, Duniyar ilimi ta tabbatar da cewa mafi yawancin mutane abin su bai wuce inci 5 ko 6. Masu inci 15 a duniya tsiraru ne. Yayin da mutum ke yawan tunani akai, zai raina abin shi wanda hakan na iya haifar da Koro Syndrome.

Wallahi karya ne, ba wanda ya isa ya sace maka azzakari sai dai in wuka yasa ya yanke.

Wasu na nuna bidiyo na wasu da suka ce sun sace ma wani, amma ko a bidiyon za ka gane tabbas “KORO SYNDROME” ne ya kama wanda aka ce an sace mawa.

Allah ya kyauta.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button