Maganar ɗaga kwalli akan matsalar tsaro : Ban cewa masu yi jahilai bane amma ni ba jahili bane, bazanyi ba – inji sarkin waka
Ban cewa masu yi mahaukata bane amma ni ba mahaukaci bane
Fitaccen mawaƙi a Najeriya, Naziru Sarkin Waƙa ya ja kunnen masu matsa masa da ƙiraye-kirayen sai ya ɗaga kwali mai ɗauke da “Arewa Mu Farka” yayi hoto ya ɗora a social media domin nuna damuwarsa akan halin tsaro da Arewa ke fama da shi yayi wannan kiran ne inda ya wallafa a shafin na sada zumunta sarkin waka san kano
Ga abinda yake cewa a wannan faifan bidiyo:
Ya ce zuwa yanzu kanshi ya waye, kuma ya kamata jama’a su farga su gane cewa zuciyar Shuwagabannin ƙasar ta riga ta bushe ta ƙeƙashe ba tausayi ba imani a ciki, babu wani tasiri da zanga-zanga ko daga kwalin zai yi masu a wannan lokaci, ba zasu sauya komi ba, “Shuwagabannin da sai da suka yi ɓarna wajen neman mulki, sai da sukayi ɓarna a lokacin zabensu to ta ina kuke sa ran za su saurara mana”
“Idan an fito neman yanci ko a mutu ko ayi rai ne, da haka ake samun yanci idan kun shirya nima na shirya amma duk wani abu saɓanin wannan to kada ma ku saka ni ciki don ba zan yi ba, ban ce masu yi jahilai bane amma dai ni ba jahili bane, kuma ban ce masu yi mahaukata bane amma dai ni ba jahili bane” inji Naziru
“Yanci itace ce da jini ake shayar da ita idai daga kwali ne dan Allah kar wanda ya kara yimin magana, mai ɗagawa ya ɗaga wanda bayayi ya daina, sa’a nan kuma wanda yasan amfanin kuma ya ɗaga amma wanda baisan amfaninsa ba ku kyaleshi.
Sarkin waka ya kara da cewa
“Malaman Addini wadansu bance duka ba sune sunka barku cikin halinda kuke ciki a yanzu ku cigaba da girmama su baza’a fita daga cikin abinda ake ciki ba, akwai malamai na Allah waɗanda sunka yi ta magana har sunyi shiru ,amma dan siyasa zai ɓata abu dubu amma dan siyasa yayi abu daya kaga malami na yabo sa a ina ya cancanci yabo”- inji sarkin waka.
Akwai sauran bayyanai wanda zakuji daga bakin mawakin a cikin bidiyon nan.