Legas: An yanke wa shugaban cibiyar kula da lafiya daurin rai-da-rai bisa yi wa ƴar uwar matarsa fyaɗe


Wata Kotun hukunta laifukan fyaɗe da rigingimun cikin gida da ke Ikeja ta yanke wa Daraktan Cibiyar kula da Ciwon Kansa, Dokta Olufemi Olaleye, hukuncin daurin rai-da-rai har ninki biyu a gidan yari bisa laifin lalata ƴar uwar matarsa.
Daily Nigerian Hausa na ruwaito,Mai shari’a Rahman Oshodi ya samu Mista Olaleye da laifin lalata da fyaɗe ta hanyar jima’i ga yarinyar.


Gwamnatin jihar Legas ce ta fi shigar da ƙarar mai ɗauke da tuhume-tuhume biyu.
Alkalin ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da gamsassun Olaleye ya aikata laifin.
Mista Oshodi ya ce shaidun da ake tuhumar daraktan gamsassu ne.
Wani labari: Jarumar Nollywood, Tonto Dikeh ta sauya sheka zuwa APC
Jarumar Nollywood kuma mataimakiyar ƴar takarar gwamnan jihar Rivers a jam’iyyar, ADC, Tonto Dikeh, ta koma jam’iyyar APC.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin kafar sadarwa na jam’iyyar APC a jiya Litinin.
Misis Dikeh ta samu tarba daga shugabar mata ta APC ta kasa, Mary Alile, da mataimakiyar sakatariyar yada labarai ta kasa, Duro Meseko, a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Sanarwar ta ce: “Fitacciyar Jarumar Nollywood Tonto Dikeh ta koma APC.
“Tonto Dikeh, wacce ita ce mataimakiyar dan takarar gwamnan jihar Rivers a zaben 2023 a jam’iyyar African Democratic Congress, shugabar mata ta kasa, Dr Mary Alile da mataimakiyar sakatariyar yada labarai ta kasa, Hon. Duro Meseko su ka karɓe ta a shelkwatar Jam’iyyar.”