Labarai

Labari mai daɗi : zamu biya N-power “batch C” kudin wata 8 – Dr. Betta edu

Mun binciko kudaden N-power kaf, za mu biya ku albashinku na wata 8 da kuke bi kwanannan – Ma’aikatar Jin kai ta yi wa ma’aikatan N-power albishir mai daɗi

Ma’aikatar jin kai da kawar da talauci a Nijeriya, ta bayyana nasarar kammala binciko kuɗaɗen Ma’aikatan N-power bayan, ta sanya wasu kwararru kan harkar binciken kudi sun tattaro masu bayanai game da kuɗaɗen albashin Ma’aikatan

Labari mai daɗi : zamu biya N-power "batch C"  kudaden wata 8 - Dr. Betta edu
Labari mai daɗi : zamu biya N-power “batch C” kudaden wata 8 – Dr. Betta edu Hoto/facebook: Pg

Mr Akindele ne ya bayyana hakan, lokacin da yi zama na musamman da wasu daga cikin Ma’aikatan N-power, kamar yadda ministar jin kai Dr Betta Edu ta tabbar wa Katsina Daily News

“Labari mai daɗi da nake son bayyana maku a nan shi ne, kuɗaɗen an kammala binciko su a jiya, kuma za ku sami hakkokan da kuke bi, ba tare da wani bata lokaci ba. Za a fara biyan ma’aikatan N-power yan rukunin C dake bin bashin kusan watanni 8 ba da wani dogon lokaci ba.

Ya kuma bayyana cewa ministar jin kai Dr Betta Edu na matuƙar fafutukar ganin, duk wasu hakkokan da suka rataya kan hukumar na N-power da sauran muhimman kuduroran shugaban kasa Tinubu na kyautata rayuwar al’umma, an aiwatar da shi yadda ya dace ba tare da wani jinkiri ba.

Ta kuma bayyana cewa ba tare da bata lokaci ba za a kaddamar da wani sabon shirin N-power da za a dauki sama da mutum miliyan biyar kafin karshen mulkin Shugaban kasa Tinubu.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button