Labarai

Kwankwaso ya gargadi ma’aurata su guji duba wayoyin juna

Dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kira ga ma’aurata su guji duba wayoyin junansu domin kauce wa samun sabani a zaman aure.

Ya yi kiran ne ranar Asabar a lokacin walimar da gwamnatin jihar Kano ta hada ta bikin ‘auren zawarawa ko auren gata’ da ta gudanar a birnin na Kano.

A ranar Juma’a ne gwamnatin Jihar Kano ta daura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 da ta dauki watanni tana shiryawa, a shirinta na kawo ci-gaba da kyautata zamantake tsakanin al’ummar jihar.jaridar TRTAFRIKA Hausa na ruwaito.Kwankwaso ya gargadi ma'aurata su guji duba wayoyin juna

Ranar Asabar kuma gwamnatin ta shirya gagarumar walima wadda manyan mutane daga fadin kasar — wadanda suka hada da gwamnoni da malamai da ‘yan kasuwa da sauransu — suka halarta

Manyan baki sun gudanar da jawabai daban-daban domin jinjina wa gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matakin da ta dauka na aurar da mutum 1,800.

A jawabinsa, Sanata Kwankwaso, wanda ya soma gudanar da auren zawarawa a lokacin da yake shugabancin jihar ta Kano, ya gargadi sabbin ma’auratan da su yi biyayya ga dokokin Musulunci wajen tafiyar da harkokin aure.

“Ina kira a gare su (ma’aurata) su kasance mutane masu bin tsarin aure kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Kuma lallai su kula sosai kada su yi wani abu da zai sa wannan aure na gata ya samu matsala.

Akwai shawara iri dubu da mutane za su iya ba ku, kuma na san da ma an soma ba ku, kuma za a ci gaba da ba ku. Malamai za su fadi nasu, ‘yan kasuwa da sauransu za su fadi nasu,” in ji Sanata Kwankwaso.

Ya kara da cewa: “Zan ba su shawara daya: yanzu Allah ya kawo mu wani zamani na waya. Kusan kowa yana da waya. To, kowa ya kiyaye wayar mijinta ko matarsa domin yanzu suna cikin matsaloli da ake samu a aure a wannan kasa tamu da ma duniya baki daya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button