Kuma : Barayi Sun Kuma Sace Dalibai Biyu Na Jami’ar Tarayya Dake Gusau


Wasu ‘yan bindiga a daren ranar Asabar sun sake yin garkuwa da wasu daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara.
Daliban biyu, a cewar wani shaidan gani da ido, namiji da mace ne, wadanda aka yi garkuwa da su a dakin kwanan daliban da ke kusa da jami’ar da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar a unguwar Sabon Garin Damba da ke Gusau, babban birnin jihar.


Jaridar Dimokuraɗiya na ruwaito mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummar ne ‘yan mintoci kadan bayan karfe 8 na dare inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi don tsorata mazauna yankin.
Jami’an tsaro sun yi ta harbin bindiga da dama inda suka yi kokarin fatattakar ‘yan ta’addar amma ‘yan fashin sun tafi da dalibai biyu.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa hada jami’an tsaro na ‘yan sanda da sojoji a halin yanzu suna bin ‘yan fashin.
Kokarin yin magana da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, bai yi nasara ba domin bai amsa kiran da aka yi masa ba.
Duka dai baifi wata daya da barayin dajin suka shiga wajen kwanan dalibai mata na Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau din inda suka kwashi daliban da har yanzu ba’a san adadinsu ba suka tafi dasu.
Gwamnatoci da suka hada da ta Jaha da ta Tarayya sunsha alwashin kubutar da daliban daga hannun yan bindigar amma abin yaci tura.