Kidaya challenge: Murja kunya tayi muguwar addu’a ga duk wanda ya shiga gasar Rarara
A yan kwanan mutane yan gwagwarmayar da matasan malamai masu amfani da kafar manhajar titkok sunyi wa shahararren mawakin nan adamu Dauda kahutu rarara wankin babban bargo irin halin da kasa take ciki amma yazo yana mayar da yara mabarata da yan maula akan gasa.
Kida challenge wani gasa ne da ya sanya akan kidaya da za’a a shekara mai zuwa wato 2024 shine yayi waka ya sanya gasar ta inda yan tiktok sunkayi masa tawaye, itama murja kunya ta shiga sahun masu kira da kada ayi wannan gasar ga abinda take cewa.
Murya kunya ta wallafa wannan faifan bidiyo akan shafinta na tiktok mai suns yagamen1
“Ya Allah dan matsayin manzon Allah s.a.w duk wanda ya hau wannan gasa “kidaya challenge” da aka kawo a cikin arewar nan wai kidaya Allah Ubangiji ka debe masa albarka, Allah ka hana shi cin yau dana gobe , Ubangiji Allah mu kuma ka bi muna hakkin mu.
“Muna cikin wani yanayi masifa kashe kashe da bala’i da sace sace da sauransu, Allah yasa duk wanda ya hau wannan gasar ta kidaya daga an kidaye shi anka tantance shi sai sambisa.inji murja kunya
Ga bidiyon nan ku kalla.
@yagamen1????????????????♬ Love You So – The King Khan & BBQ Show
Mutane sunyi martani a karkashin wannan bidiyo.
@mrskabeer cewa take:
Ameen ya rahman wannan rainin wayo ne da rainin hankali Allah yay mana maganin su.
@hannatulawan483 abinda take cewa:
Allah mahakaciya yar gidan Ibrahim kina raba aljana ne ko Ibrahim yana rabawa.
@sadiya’yar’lele abinda ta rubuta kenan:
da rara da masoyansa Allah y debe musu albarka Dan darajar shugaban S A W AMEEEEEN
@MAAWIYYA ga abinda yake cewa:
BAKAR ADDU’AH tana afkawa kan wanda ya yi ta da hanzari.
@Musbancy abinda yake cewa:
Ni wlh Baki taba abin da ya burgeni ba
irin na wannan lokaci