Karba musulunci : Aisha sulaiman ta samu aiki a gwamnatin tarayya da makudan kudi da kujerar hajji
Biyo bayan videon da Zinariya ta yaɗa wa duniya na A’isha Sulaiman ƴar ƙabilar Ibo da ta karɓa addinin Musulunci, Musulmi a faɗin duniya sun kaɗu tare da tabbatar mata da cewa tana da gata inda suka tallafa mata da taro da sisi domin ganin sun cika mata burin ta na samun aiki ko jari domin fara sana’a.
Sakin bidiyon ke da wuya, wani babban mutum mai riƙe da madafan iko a Najeriya ya tuntuɓi Zinariya inda aka tabbatar mishi da gaskiyar lamarin. Nan take ya wa A’isha Sulaiman albishir da samun aiki da gwamnati tarayya. A cikin kwanaki uku, A’isha Sulaiman ta karɓa takaddar kama aiki da wata babbar ma’aikatar ilimi a ƙarƙashin wata jam’iar gwamnatin
tarayya a jahar ta.
Ga A’isha nan riƙe da shedar kama aiki tare da wakilan Zinariya.
Bayan haka, A’isha Sulaiman ta samu tallafin kuɗi fiye da yadda ake tsammani domin fara kasuwanci.
Har wa yau, wata baiwar Allah wacce bata so a ambaci sunan ta ba ta canja wa A’isha Sulaiman kayan ɗaki baki ɗaya tare da yi mata tayel da fentin ɗaki kai ka ce amarya ce. Ta siya mata sabbin kujeru, injin wanki, firiji, gado, katifa, tukwane da duk wani abu da ka san ana wa amarya.
A’isha har wa yau ta samu kyaututtuka daga wajen mutane a jahar Bauchi da faɗin Najeriya da ƙasashen ƙetare. Har da muke wannan rubutun tana ci gaba da samun tallafi.
A irin bayanan da muke da su a hanu, ba abun mamaki bane ku ga A’isha Sulaiman a ɗakin Allah a Hajjin bana idan abu ya tabbata.
Ko ma dai ya ta kaya, za ku ji kuma zaku gani.
Ga wadanda suka yi alkawari, Allah basu damar cikawa.
Muna godiya matuƙa ga dukkan waɗanda suka taimaka da taro da sisi. Allah saka muku da alheri. Kuma Allah faranta muku kamar yadda kuka farantawa A’isha Sulaiman.
Uwa uba, muna godiya ga mabiya Zinariya da suka dinga sharing videon A’isha Sulaiman har ya kai ga inda ake so. Allah sakawa kowa da alheri.
Ga bidiyon nan.