Kannywood

Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya!

Mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara, ya sanya gasar wata sabuwar waka da yayi akan shirin gwamnatin tarayya na ƙidaya da za’a gudanar a farkon shekarar 2024, inda ya bayyana muhimmancin ƙidaya ga yan ƙasa Nigeria.

Aisha Humaira wacce abokiyar aikin Rarara ce, tayi bayanin yadda ƙidayar za ta taimaka a sha’anin tsaro, tare da bayani akan yadda gasar za ta kasance da kuma irin kyaututtukan da za’a bayar ga wadanda suka shiga gasar, da suka hada da Mota, Babur da kuma kuɗi.

Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya!
Jaruman TikTok sun yiwa Rarara bore akan gasar wakar ƙidaya!

Sai dai kuma gasar bata samu karɓuwa ga ma’abota shafukan sada zumunta musamman TikTok ba, inda wasu jaruman dandalin ke ganin Rarara bai shiga lamarin kira ga gwamnati akan matsalar tsaro da ake shan fama a Arewacin Nigeria ba, saboda haka a yanzu shima ba zasu karɓi bukatarsa ba.

Wani labarin : Kidaya challenge: Rarara kaji tsoron Allah – Abis fulani

Kidaya abu ne mai muhimmanci sosai nayi maganar sa kafin a daga shi kuma babu wanda ya bani ko sisi nayi wannan bidiyo a baya , to yanzu ma zanyi bidiyo na magana daban akanshi Rarara wallahi billahi azim kaji tsoron Allah, dan Allah dan annabi ka dunga saka tunanin mutanen arewa kafin kayi wani abun lokacin siyasa ya wuce.

“Yanzu ya kamata kayi abinda yan uwanmu da mutanen zasu cigaba fisabilillahi ana tsaka da kashe kashe mutane ana sace yan uwanmu da iyayen a daji amma babu abinda ka saka muna sai da yiwa tinubu waka wai baba tinubu yan arewa na godiya da kake nunawa duk abinda ya shafi yan arewa baya gabanka, inda ba abin neman kuɗi bane.

“Abis fulani ya kara da cewa da farko baka taba waka ka nunawa shuwagabanni nan matsalolin da arewa ke fuskanta ba.

Bugu da kari ba’a dade da munkayi kamfin din arewa mufarka ba manya sananu “celebrities” irinsu Ali Nuhu sunka fito sunkayi magana amma kai ƙus baka ce komai ba, saboda kana tsoron kayi magana suki baka aikin waka nan gaba.”- inji abis fulaniMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button