Jami’an tsaro sun kama wata ƴar tiktok da ake zargin kalamai na tada hankali
A cikin wani labari da gidan rediyo Freedom Radio kano sunka kawo rahoto akan wata yarinya yar Tiktok wanda tayi sakin baki aka zage zage da dura ashariya akan tayar da hankali na cewa tabbas zata iya kunar bakin waka .
A manhajar titkok ta tara mutane da dama akwai na ariziki akwai na tsiya wanda tabbas akwai abubuwa da dama da suke aikatawa, wannan labarin wata yarinya ce Firdausi yar unguwar dan dushe da ke kano wanda a jiya iyayenta da yan uwanta basu yi barci ba yadda Sunka ga safiya haka Sunka ga dare shine nan take Mahaifiyar yarinyar da yayarta suke rokon mahukunta da shuwagabanni da a yafi mata a sakota ko yanzu ta gane shayi ruwa ne ga abinda mahaifiyarta ke cewa.
“Jiya ne da dare aka hauro mana gida anka shigo anka tafi min da yarinya sakamakon tiktok da tayi ina roko dan Allah nidai a dawomin da yarinya ta tayi kuskure, dan Allah dan Annabi ina rokon shugaban dss dan Allah tayi kuskure.”
Wannan dai shine rokon su ga shuwagabanni kuma wannan kira ne ga al’umma da su shiga taitayinsu na sakin baki.