Labarai

Gaskiyar zancen wannan baiwar Allah da anka kama da harsashe da bindiga guda biyu a katsina

Kwanan baya an samu yaɗuwar labarin matar da anka kama da bindiga da albarusai a jikarta ankace tana yiwa yan bindiga safara ne ashe ba haka bane ita matar soja ce sun samu sabani ne ta dauki jakarsa maimakon tata kamar yadda shafin zinariya tv na ruwaito a shafinsu na Facebook.

Bisa ga bayanai da muka samu Ita wannan baiwar Allah Matar Soja ce ta baro Bauchi ne saboda sun samu Hatsaniya da shi Sojan sai ta ɗauki Jakarsa ta zuba kayanta a ciki ta kamo hanya ta baro masa ƴayan su ba tare da ya sani ba, kuma a rashin Sa’a tabar wayarta a gida ba tare da tasan wayar bata jikinta ba saida tazo Katsina An ajeta a tasha kuma a Lokacin ana binciken kowaye yazo tasha zai shiga mota ne ko zai hau sai an bincikeshi.Gaskiyar zancen wannan baiwar Allah da anka kama da harsashe da bindiga guda biyu a katsina

Shine ana duba kayanta a ka ga waɗannan 2 Magazine ɗin kuma ita bata san dasu ba saida aka nuna mata aka tambaye ta wannan pa tace bata san dasu ba aka garzaya wurin ƴan Sanda don faɗaɗa bincike nan aka san cewa Wurin yayarta tazo a nan Katsina aka tambaye ta wayarta a nan ne tasan tabaro wayar a Bauchi, sai ta faɗi unguwar da Aunty ta take da kuma sunanta akaje aka faɗawa Aunty ta tazo wurin.

A kayi bincike sosai, sai rikici ɗin ya koma wurin Sojojin Katsina Saboda Ita Aunty ta, ta kira mijin Yarinyar ta faɗa masa shi kuma dole yaje yakai “report” a don yasan da waɗannan bullets ɗin a cikin jakar, shine aka kira Sojojin Katsina suka anshi rikicin ɗin.Gaskiyar zancen wannan baiwar Allah da anka kama da harsashe da bindiga guda biyu a katsina

Kawo yanzu dai Mijin nata yana tsare Saboda sakacin da yayi na barin Harsasai a gidan har hakan tafaru Allah ya kyauta gaba ya bashi mahita Amin.

Gaskiyar zancen wannan baiwar Allah da anka kama da harsashe da bindiga guda biyu a katsina
Wadda anka kama da bindiga

Muna ƙara Addua duk wanda yake da sa hannun wajen hana Al’umma zaman lahiya Allah ya kama shi kowane ne, Allah ya san su mu bamu sansu ba muna roƙon Allah ya tona masu Asiri Allah ya kamasu irin kamun shi Alfarmar Sayyadina Rasullullahi Sallallahu Ta’alah Alaihi Wasallam Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA