Labarai

Gaskiyar magana akan matar da Mijinta ke sanyawa sasari “ankwa” a potiskum

Labarin wamnan baiwar Allah da yayi fice a soshiyal midiya inda ake zargin wani bawan Allah ya munana rashin tausai da kwantatawa mai dakinsa wanda yanzu haka jami’an tsaro sunka yi nasarar cafke wannan bawan Allah.

Wani mutum mai amfani da kafar sada zumunta ta Facebook Idriss Zakari Yobe ya samu zuwa gidan wannan bawan Allah domin jin sahihin labarin abinda yasa yake aikatawa matarsa hakan inda Idriss Zakari Yobe ya wallafa tattaunawa da yayi da iyalan malam Muhammad mai waldan- robobi ga yadda zan tawarsu ta kasance.

“Yau 05/October/2023 Na ziyarci anguwan Dabo Aliyu Stadium inda na zanta da wasu daga cikin al’ummar wannan anguwa kuma na zanta da family’s wannan bawan Allah.

Shidai Wanda Ake Zargi Sunansa Mal Mahammadu Mai (Waldan-Robobi)Abinda ɗiyar sa mai suna sadiya Mahammadu ta shaidamin cewa mahaifinyarsu tana fama da laluran tabin hankali wanda wannan lalura ya jima tana fama dashii inda tacemin itama ta tashi taga mamanta da wannan cuta.Gaskiyar magana akan matar da Mijinta ke sanyawa  sasari "ankwa" a potiskum

Amma a yanzu wannan matsala ta karu ta yadda inhar mama ta fita waje bata dawowa gida sai dai an nemota wani lokaci munashan wahala kafin musan inda take ganin haka baban mu ya yanke shawaran in zai tafi kasuwa yana sa mata ankwa a kafanta sbd gudun karta fita sai bayan ya dawo zai kunceta.Gaskiyar magana akan matar da Mijinta ke sanyawa  sasari "ankwa" a potiskum

Na tambayii Sadiya ko kuna da matsalan abinci.? Ta cemin a gaskiya babanmu yana iya kokarin sa wajen bamu abinci daidai iya Karfinsa Alhamdulillahi.

Sadiya tamin tambaya kamar haka.?
Yaushe babanmu zai dawo ne.?
Zai dawo da zaran jami’an tsaron sun gama binciknsa insha Allahu.

Wannan suna kalaman da na tattauna da iyalan Mal Mahammadu Mai (Waldan-Robobi).”

Ga bidiyon hirar nan.

Nidai abinda na fahimta Mal Mahammadu mutum ne mai karamin karfii ta yadda bazai iya daukan nauyin jinyar matar sa ba duba da irin sana’ar da yakeyii da kuma yadda nasamu family sa sannan kalmar da ake la’antar da ake masa bisa zargin cutarda iyalinsa wannan ba gaskiya bane sbd ga abinda ɗiyar sa ta shaidamin.

Amadadin al’ummar Potiskum LGA muna neman agajin Shugaban hukumar bada agajin gaggawa YOSEMA Dr Mohammed Goje da taimaka ya dauki nauyin jinyar matar Mal Mahammadu Mai (Waldan-Robobi) ataimaka ma iyalansa da abinda zasucii.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button