Datti Assalafy ya sake yin tumu-tumu da Rarara a sabon martani
Shahararren marubucin nan kuma masoyin Buhari Datti Assalafiy ya sake yiwa rarara wankin babban bargo wanda yake karyata shi tare da kiransa mahaukaci a shafinsa na sada zumunta ya wallafa hakan.
Mulkin Watanni uku na azabar yunwa da tsadan rayuwa da yunkurin haifar da yaki tsakanin ‘yan uwan juna na addini da jini (Nigeria da Nijar) bai fi shekaru Takwas na Mulkin Buhari ba, karya kake dakikin mawaki mahaukaci
Hakika bamu taba yin nadamar zaben Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Nigeria ba, kuma yayi kokari mun gani koda a fannin yaki da BoKo Haram ne, mawaki ka sani cewa ko kura tayi mushe tafi karfin kallon raini, kabi a hankali dan kaniyarka domin har yanzu akwai ‘yan gani kashenin Buhari a cikin wannan Gwamnatin, zasuyi maganinka
Shugaba Buhari ya karbi Nigeria a lokacin da kaso mai yawa na Kananan hukumomi a Jihar Borno da Yobe suna karkashin ikon Boko Haram, idan kwakwalwar kifi kake dashi ka manta to mu da muke da kwákwaIwar mutane bamu manta ba
Mun shaida ganin lokacin da Musulmi zai shiga Masallaci a bishi da b0mb a kashe shi, a lokacin tashar motoci da kasuwanni da Masallatai na Arewa sun zama dandali na tayar da b0ma-b0mai ana ka$he Musulmai
Amma saboda kudi yau wani banza dan iskan mawaki zai tara ‘yan jaridu ya biyasu Miliyoyin Naira yace wai Mulkin wata uku yafi mulkin Shekaru takwas na Buhari wanda ta kawar mana da masifar Boko Haram, amma wannan mawaki ya kai tattaccen dan iska marar imani
Kuma naji yana cewa wai tsohon IGP ya janye masa ‘yan sanda masu tsaronsa don ‘yan Kwankwasiyya su kashe shi, to kai a wa? don ‘yan Nigeria sun rasaka sai me? dama ma me kake tsinana wa ‘yan Nigeria imbanda ‘yan siyasa su sato dukiyar talakawa su baka? baka da wani amfani, domin kai burgu ne wanda ake sato dukiyar talakawa a baka ka cinye
Tsohon IGP Alkali Baba Usman yayi daidai da ya janye maka ‘yan sanda domin baya cikin ka’ida, Nigeria bata kan saiti ne shiyasa ake daukar maroka jahilai a matsayin wasu mutane masu daraja har a basu jami’an tsaro a lokacin da talakawa dubbai suna bukatar a basu tsaro
Allah Ka gyara mana Nigeria