Kannywood

Dalilin da yasa nake yawan fitowa tantiri a fim – musa mai sana’a

Mutane da yawa suna yawan mamakin miyasa musa mai sana’a yake yawa fina finai akan tsinuwa wanda yaka baiwa mutane mamaki akan wannan jarumi.

To a karshe dai a cikin shirin gabon talks show room anyiwa jarumin wannan tambaya kuma yayi bayanin abinda yasa yake yawan wadannan fina finai.

Dalilin da yasa nake yawan fitowa tantiri a fim  " - musa mai sana'a
Dalilin da yasa nake yawan fitowa tantiri a fim ” – musa mai sana’a Hoto/Instagram:Musa mai sana’a

Kina uwa bazaki tsaya ga sana’ar ta gida ba da keji abu ya samu a makota yanzu kina tashi bazar bazar Assalamu ashe haka abu ya faru ba addu’a za’ayi ba Allah ya kiyaye ba sai ayi firar abinda ya faru, sai a fara eh wallahi ae karuwanci take nifa na ganta da mota nifa na ganta da kaza sai ayi ta tattauna abinda bai shafeku ba, ku ƙi fadar alkhairi.

To Shikenan ‘ya’yanku na gida sai su tashi da fadan alkhairi dalilin yin irin yawan fina finan kenan babanmu ne yake yawa tsinewa ‘ya’yan mutane duk abinda ankayi bazai ce Allah sa albarka ba, itama babarmu (mahaifiyarsa) tana tofa albarkacin bakinta ba addu’a ba Allah sa albarka, to ya ɗa ana tsine masa bazai tsine bazai kama shi ba bakin iyaye.

To dalilin yawan wadannan fina finai kenan saboda idan lyaye sun gani su guji la’antar ya’yan wasu da kuma ‘ya’yansu –inji mai sana’a

An sake yiwa jarumin tambaya minene burkina a Kannywood?.

Bai wuce in gama lafiya ba, yadda na shigo ta lafiya in ƙara lafiya ba daukar magana in jawa kaina abin tsegumi shine ni burina kar n abarwa bayana abin fadi burina kenan, Sa’a nan ni in gama lafiya.”-inji Musa mai sana’a

Ga bidiyon nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button