Dakta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi Na Buƙatar Taimakon Gaggawa – Imam Aliyu Indabawa


A yanzu nan wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta ta Facebook Imam Aliyu Indabawa ya wallafa wannan bayyani a shafinsa na sada zumunta akan maganganun sheikh Dr abdulaziz Dutsen tashin inda yake cewa.
Ina kira ga iyalan Malam Idris, ƴan uwansa da almajiransa da su yi gaggawar ɗaukar Malam zuwa asibiti domin nema masa lafiya. Zancen gaskiya Malam na buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa ba wai maganar cin fuska ba.


Duk me lafiyayyen hankali ya san abubuwan da Malam ya ke yi sun wuce neman suna sun ci karo da ƴantaccen hankali, musamman ma maganar da ya yi kan Falasɗinawa, da idona na kalli bidiyon yanzu haka ina da shi a wayata.
Sannan Malam kullum ba shi da aiki sai zagi da cin mutuncin mutane masu mutunci. Yadda ya ke gani duk Nijeriya babu malamin kirki sai shi kaɗai, shi ya sa ya ke cin zarafin malamai a mumbarinsa son ransa. Duk wata fitina da za ta janyo a yi ta cece-ku-ce Malam Idris sai ya taso da ita.
Ka duba ƙoƙarin da su Bala Lau da Sheikh Abdulwahab Abdallah suka masa don ganin an fito da shi daga Kurkuku, amma mutumin nan yana fitowa sai ya hau kansu ya ce Allah ya isa tsakaninsa da su.
Ina mamakin masu zama a gabansa yana wannan hauragiya da kuma masu ba shi kariya, ko da ya ke an ce mutum ne mai arziki kuma yana kyautata wa almajiransa shi ya sa su ke binsa ido rufe.
Allah shiryi Dr. Idris ya ba shi lafiya.
Hausaloaded ta samu tattaro martanin mutane akan wannan rubutu.
@Nifsu Hayat cewa yake :
Zancen Dr. Yace baya tare da palestine wannan zancen qarya ne, na saurare karatun kuma sam banji inda yace haka ba. Ku dinga yiwa bawan Allah nan adalci, don yayi katobara wasu gurare bashi zaisa amasa qazafin abinda baiyi ba. Allah ya shiryemu duka
@ahmed Na’abba cewa yake :
Sannan ya zama wajibi hukunta ta dauki mataki domin daga irin wannan maitatsine ya fara har takai da fara yanka mutane da garkuwa da su. Ya rage na hukuma.
@Yusuf ahmad cewa yake :
Gaji Wawan banza Kaine kake neman taimakon gaggawan meye yafada na rashin hankali in ka isa kasa Mana video din dayayi maganar rashin hankalin
@naziru Aliyu Ibrahim cewa yake:
Nima nayi wannan tunaninin domin duk mai daawar sunna yasan wannan abjn da yake ya sabawa kaida ta salafiyya . allah ya daidaito da hankalinsa ko don mabiyn sa.
@herfiez Muhammad cewa yake :
Wallahi inada audion tun daga farko har karshe kaji tsoron Allah kasa ma kowa ya gani Wanda yakai kusan awa daya da wani abu.