Labarai

Budurwa yar Najeriya tayi wuff da dan koriya , bidiyon bikin ya tayar da kura

Wani mutumin kasar Koriya da ya auri Bayarabiya ya kayatar da mutane da dama a ranar aurensa yayin da ya yi shigowar kasaita tare da yan uwa da abokansa.

Gaba daya abokan angon sun sanya babbar riga yayin da suke rawan wakar Yarbawa ta Asake Omo Ope.

Ango dan Koriya ya tashi kan jama’a a wajen aurensa
Angon ya kasance cikin farin ciki tsatsa yayin da yake kada hannaye da kafafuwansa majiyarmu ta samu labari daga jaridar legit.

 

Budurwa yar Najeriya tayi wuff da dan koriya , bidiyon bikin ya tayar da kura
Budurwa yar Najeriya tayi wuff da dan koriya , bidiyon bikin ya tayar da kura Hoto/tiktok

Mutane da suka ga yadda angon ke kokarin rawa sai kace dan Najeriya sun ce lallai ya shafe tsawon kwanaki yana bita don burgewa.

Ya rera wasu baitukan wakar yayin da sauti ya karade dakin taron. Ya kasance cike da kuzari da kwalisa yayin da ake masa yayyafin dala.

Shafin @teamdfams ne ya yada bidiyon nasa.

Ga bidiyon nan.

@teamdfams Korean Groom, Nigerian Traditional Wedding.. No Problem!#weddingtiktok #nigeriantiktok #nigeriantiktok #weddingvideo #nigerianwedding #koreanwedding ♬ Omo Ope (feat. Olamide) – Asake

Mutane sunyi martani a karkashin wannan bidiyo inda sunka tofa albarkacin bakinsu:

OLA ya ce:

“Allah kadai ya san kwana nawa ya kwashe yana bita kafin ranar auren.”
Your girlfriend ta ce:

“Awwwnn wacece ta auri lee min hoo.”
maryanneyusuf ta ce:

“Shin ni kadai ce nake murmushi yayin kallon wannan.”
osasonayemi ya ce:

“Barka da zuwa gida Adebowale.”
Sophie_face_’n’_spa ta ce:

“Kaina yana ta tashi. Ina taya wannan matar da aka yi aurenta murna.”
Michellentee ta ce:

“Don Allah ku dunga karin bayani ina bukatar miji dan Koriya nima.”
Reineer Velasquez ta ce:

“Surankan da ke baya sun ga kudi.”
Actress Diamond1 ta ce:

“Kun fara kuma wacece ta je ta auri wanda nake mutuwar so.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button