Baya ta haihu : Kamfanin BUA ya yi karin farashin kayan abinci a sirrance
Biyu ga wannan watan Oktoba ne kamfanin BUA siminti sunka cika alkawalin rage farashin siminti inda a yanzu nan wasu garuruwa sun samu sausauci amma wasu kam babu wannan sasauci har yanzu.
Majiyarmu ta tabbatar da hakan ne saboda a nan Sokoto ana sayar da buhun Siminti 3,900 saɓanin 4,200.
Yanzu nan muke samun wani labari wanda baida daɗin ji inda jaridar Dclhausa na ruwaito cewa baya ba zane inda anka kara farashin abinci wanda inda sunka ruwaito labari.
“Kwanaki kadan bayan sanar da rage farashin buhun siminti, kamfanin BUA ya yi ta karin farashin kudin kayan abinci irinsu buhun sukari da na garin fulawa da kuma katan din taliya spaghetti, kamar yadda wani bincike ya nuna.
Hukumar gudanarwa ta kamfanin na BUA a ranar 1 ga watan Oktoba ta sanar da rage farashin buhun siminti zuwa Naira 3,500 kan kowace buhu.
Sai dai har ya zuwa wannan lokaci yan Nijeriya na guna-gunin cewa sabon farashin siminti bai fara aiki ba a kasar domin ko kobo ba a rage ba har yanzu.”