Bamu janye ɗaukaka ƙara akan shari’ar zaɓen gwamnan Kano ba – INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta musanta cewa ta janye ɗaukaka ƙarar da tayi akan shari’ar zaɓen gwamna ta jihar Kano, inda tace takardar da ake yaɗawa mai dauke da sa hannun wani jami’in shari’a na reshen hukumar dake Kano, ba takarda ce wacce ta fito a hukumance ba Majiyarmu ta samu ta majiyar gidan rediyo Nasara
INEC ta bayyana haka ne cikin wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, mai dauke da sa hannun babban kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan al’umma akan zaɓe, Sam Olumekun, inda ta bukataci al’umma da suyi watsi da waccan jita-jita da ake yaɗawa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, tuni hukumar ta bawa lauyoyin ta dama akan suyi dukkan abinda ya dace, wanda bai ci karo da tsare-tsaren ta ba.
A wani labari :Mu yan kallo ne akan rikicin zargin takardun bogi tsakanin Tinubu da Atiku – NNPP
Jam’iyyar NNPP ta ƙasa, ta ce bata da hurumi akan batun zargin takardun makaranta na bogi da dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya ke yiwa shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, inda ta ce nata Ido ne a cikin lamarin.
Jawabin hakan ya fito ne daga bakin mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Nwaeze Onu, a ranar Juma’a, inda ya ce NNPP bata shigar da ƙara kotu ba, saboda haka bai kamata a yanzu ta dauki bangare ba, kawai dai su na kyautata zaton kotu za tayi aikin ta.