Ayiriri : Rahama Mk, Hajiya Rabi mai kada ta kwana Casain ta haihu
Hajiya Rabi Bawa Mai Kada Jarumar Fina Finan KannyWood (Rahama MK) Ta Cikin Shirin Kwana Casa’in Ta Haihu Na GasKe Bana Fim Ba.
Jiya Ne Muke Samun Labarin Haihuwar Jarumar. Inda Ta Haihu Cikin Koshin Lafiya, Sai Dai Da Yawan Mutane Basu San Cewa Jarumar Tana Da Aurenta Ba.
Sai Dai Mu Nan Munsha Kawo Maku Hotunan Jarumar Tare Da Mijinta Wacce Tayi Aure Sama Da Shekaru Biyu Kenan Dasu Gabata.
A Satin Nan Ne Dai A Bayyana Hajiya Rabi Bawa Mai Kada A Matsayin Wacce Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Alfawa Karkashin Jam’iyyar Guguwa Party Inda Ta Kayar Da Abokin Karawarta Na Jam’yyar Haske Wato ABM Adnan, Amma Fa A Cikin Shirin Na Kwana Casa’in.
Mansura Isah Tana. Daya Daga Cikin Wanda Su Wallafa Bidiyon Jaririn Da Rahama MK Ta Haifa A Shafin Sada Zumunta, Tare Da Tayata Murnar Haihuwar Abokiyar Aikinta Kuma Wacce Kabilarsu Daya Wato (Yoruba).
Mutane sunyi martani sosai akan wannan fustin di da mansurah Isa nayi a shafinta na Instagram.
@ana_herleemerh tana cewa ‘
Yanzu wa zai Rike Mana Alfawa Congratulations her excellency Allah ya raya.
@timerhstouch ga abinda ta rubuta:
Ahhh masha Allah tabarakallah,,,Salma tayi qanwa…Allah ya raya ta kan tafarkin sunnah.
@muhajiraismail cewa take :
Tabarakallah Masha Allah…… Congratulations Her Excellency, Hajiya Rabi … Allah shi raya baby ya dayyaba , Aamin .
@herleemertu_001 ga abinda take Cewa :
Masha Allah Allah yayiwa rayuwan baby albarka kin zama governor alfawa kin haihu afili ALLAH yasa albarka cikin rayuwan ku.
@aysha_majeed cewa take :
Alfawa is calling Allah ya raya, yarinya zata sha gata uwa gwamna uba gwamna, salma tayi kanwa.