An Kama wani mutum yana Yunƙurin Fyaɗe Ga ’Yar Shekara 85
Makwabta sun cafke wani wanda ya yi yunkurin yin fyade ga wata tsohuwa ’yar shekara 85.
Dubun mutumin mai shekaru 56 ta cika ne a yayin da yake neman zakke wa tsohuwar da karfin tsaya ayankin Uhronigbe da ke jihar Edo.
Tsohuwar ta kai ƙara ofishin ’yan sanda ne bayan makwabta sun kai mata ɗauki a lokacin da mutumin ya kutsa daƙinta ya tube, yana neman keta matuncinta.
Rundunar ’yan sandan jihar ta gabatar da mutumin ga ’yan jarida ne tare da wani matashi dam shekara 29 da ake zargi da yi wa wata ’yar shekara 18 fyade a kauyen Ehor. Jaridar Aminiya hausa na ruwaito.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya ce an kawo karar matashin ne cewa ya yi wa budurwar fyade bayan da ya yaudare ta da sunan zuwa kamun dodon koɗi, ya far mata da ƙarfi ya yi mata fyade.
Jami’in ya ce an kai ta asibiti domin duba lafiyarta.
Ya ce mutum biyun da ake zargi sun amsa laifin amma za a gurfanar da su a kotu.