Al’amarin Rarara yafi kama da masu rashin ilimi ba ƙyauyanci ba – Dr.Muhsin Ibrahim
Dr. Muhsin Ibrahim shahararren mai amfani da kafar sada zumunta kuma mai rubutu da sharhi akan al’amuran da sunka shafi masana’atar kannywood da kuma Masana’atar ita kanta.
Dr.muhsin yayi tsokaci akan irin yadda ya fahimci kalaman mawaki dauda kahutu rarara inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta kamar haka.
“Ba na alaƙanta shirmen Rarara da ƙyauyanci. Al’amarinsa ya fi kama da halayya da kuma rashin ilimi. Shi kuma ilimi, musamman wayewa, ba sai an je makarantar boko ba. Wani lokacin mu’amala da sauraren masu ilimi kaɗai ya isa – ko zai taimaka ka fahimci abubuwa da yawa na rayuwa.
Rarara ya fi mu’amala da masu ƙarancin ilimi da wayewa a da, wato ‘ƙolawa’ ƴan uwansa. Yanzu ya yi kuɗi, amma ya kewaye kansa da “yes-men”. Wa zai faɗa masa gaskiya ko gyara mai wani kuskure? Babu.
Idan na tuna sosai, ko jiya sai da ya ce wai idan ya umarci Tijjani Asase ya shiga wuta, sai ya shiga. Ka ga ke nan suna nuna masa “absolute, blind loyalty”, wato biyayya ta makanta. Ta yaya zai waye ko gyara wani kuskure?
Allah dai ya ba mu ilimi da arziƙi masu amfani, amin.”
Mutane sunyi martani a karkashin wajen sharhi akan maganar dr.
@Jaafar A sarki abinda yake cewa:
Muhsin Ibrahim, wannan tunani da fahimta taka ta samu karbuwa a kwakwalwata.
@Faisal Muhammad lawal cewa yake:
Wai menene abin mamaki don maroƙi ya juya wa wanda ludayinsa ya bar kan dawo baya? Su fa dama ba don al-umma ko ma ƙaunar ƴan siyasa suke yi ba. A’a, don aljihunsa kaɗai suke yi. Iya kuɗinka, iya sha’aninka. Da zarar zamaninka ya shuɗe, sai su tattare nasu ya nasu, su arce gurin na gaba. Dama can ya san cewa duk matsalolin da muka yi ta faɗa a kan Buhari gaskiya ne amma ya ƙi Allah saboda yana samu. Duk kyawawa abubuwan da ya faɗa a kan Tinubu yanzu, ya faɗe su a baya a kan Buhari, kuma haka zai yiwa Tinubun ma idan ya dena samu. Kare ma ya fi maroƙi amana.
@itz Ebraheem bodmerx cewa yake:
Rarara fah yana kare aljihunsa ne kawai kamar yadda dayawan Yan siyasa suke yi…..ni banga laifinsa ba…. Ko kusa bai kai Yan siyasar Nigeria butulci da shirme ba.
@surajo Abubakar Imam gangawa cewa yake :
Abin takaicin ma shine ko yanzu din ma bawai ya fusata akan halin da talaka ke ciki ba ne, dukkan alamu sun nuna takaicin sa akan rashin muqami ne da rashin damar ganin Tinubu kai tsaye
Naga ya koka akan yadda masu muqami ko ganeshi basayi sai-dai wani yayi musu describe dinsa yace… Na him sing dat song wey be Jagaba shine gaba sannan suce ohhh I understand