Abun da yasa aka yanke min hukuncin kisa a Saudiyya da kuma sanadin abinda Allah ya kuɓutar da ni – Adama Daɗin Kowa
Zuwaira Saleh Pantami, wadda aka fi sani da Adama a cikin shirin wasan Hausa mai dogon zango, wato ‘Daɗin Kowa’, wanda gidan Talabijin na Arewa 24 ke nunawa, ta bayyana yadda ta taka sawun ɓarawo a ƙasar Sa’udiyya, har aka yanke mata hukuncin kisa.
A wata tattaunawa da Dandalin Hadiza Gabon na ‘Gabon’s Room Talk Show’ ya yi da ita, Zahara’u, ko kuma a ce Adama, ta bayyana cewa an taɓa yanke mata hukuncin kisa tare da wasu mata bakwai, amma aka zartas da hukuncin kisa akan sauran bakwai ɗin, ita kuma ta kuɓuta majiyarmu ta samu labarin daga premium times hausa na ruwaito.
A cikin bayanin da ta yi Hadiza Gabon, wanda ta nuna cewa ita ba laifi ta yi ba, sawun ɓarawo ta taka, ta ce Allah ne ya kuɓutar da ita, saboda ba ta aikata laifin da aka kashe sauran ba, saboda su sauran duk sun aikata laifin da aka tuhume su da aikatawa.
Adama, wadda ta ce ‘yar’uwar tsohon Minista Ali Pantami ce ta jini, ta bada labarin yadda abin ya faru, ta ce da farko ta je Umra, amma sai ta tafi da irin tarkacen kayyayakin da ake tafiya da su daga nan Najeriya don ta sayar a can.
Ta ce, “na tafi da irin su daddawa, kuka, kuɓewa, goro da sauran su. To da na sayar sai na ga ribar da na samu har ta nunka jarin. Sai kawai da na dawo Najeriya sai na riƙa sarin irin waɗannan kaya, ina tafiya da su Saudiyya, ina sayarwa, ina dawowa ina sake saye na koma.”
Ta ce ta shafe lokaci mai tsawo ta na yin haka, har sai ranar da aka kama ta, wanda daga nan ne ba ta sake yi ba.
Yadda Na Taka Sawun Ɓarawo A Saudiyya’ – Adamar Kamaye:
Ta ce a wani zuwa da ta yi, wata rana ta na cikin birnin Riyad, sai ta yi kaciɓus da wata ƙawar ta ‘yar asalin Sudan.
Adama ta ce ƙawar ta na zaune a wani gari ne mai suna Idesa, wanda ke gaba da Riyad, inda ita Adama ɗin kan je ta na kai masu kuka, daddawa, kuɓewa da sauran su. A can ta san ƙawar, har su ka shaƙu.
“To amma fa rabon da mu ga juna an kai shekaru huɗu. Sai ta ce min ita yanzu a Jedda ta ke zaune, kuma ta je Riyad ne domin sayen kayan walimar da za ta haɗa.
“Ta ce min na tashi mu tafi, ta na gayyata ta. Abin ka da tsautsayi, shayin da na ke haɗawa ma ban sha ba. Sai na ajiye shi a firinji, na ce na ci abinci a wurin fati.
“Da muka isa gidan da take, sai na iske ƙaton bene ne, mai hawa 41. Ko lifta ma wadda ke ɗaukar mutane zuwa sama ta kai guda 25 a gidan.
“Ina zuwa ƙofar ɗaki na danna na’ura, aka buɗe na shiga. Ko hutawa ban yi ba, sai mu ka ji an sake danna na’ura, ta yi ƙara. Ina buɗewa sai ga jami’an tsaro birjik.”
Adama ta ce a nan aka tarkata dukkan matan da ke cikin ɗakin, aka yi ƙasa da su, har su takwas.
Laifin Da Ya Janyo Aka Yanke Mana Hukuncin Kisa’ – Adamar Kamaye:
Adama ta shaida wa Hadiza Gabon cewa ba ta san laifin da ta yi ba, sai ga su tsare a kurkuku har su takwas. Ta ce a can ne aka kulle su cikin ɗaki ɗaya, kuma aka haɗa su da wasu jami’an tsaron su amma masu jin Hausa.
Ta ce su na wannan zama ne dai ta riƙa cewa ita dai an zalunce ta, ba ta san laifin da aka yi ba.
“To a nan ne ƙawar tawa ta ce min gaskiya ke ba ki yi laifi ba, kin dai taka sawun ɓarawo ne kawai”.
Yadda Ƙawa Ta Ta Tsara Kisan Wani Dattijon Balaraben Da Ta Ke Aiki A Gidan Sa’ – Adamar Kamaye:
Adama ta ce ƙawar ta ashe ta yi aiki a gidan wani dattijon Balarabe har ta shirya yadda aka kashe shi, aka kwashe maƙudan kuɗaɗe da gwala-gwalai, bayan tsawon rabuwar da ta yi da ita.
Ta ce, “An ɗauki ƙawar tawa aiki a gidan wani dattijon Balarabe, wanda ba ya iya ko tafiya, sai dai komai a kan keken guragu. To ita ce ke hidimar kula da shi.
“Wannan dattijo ya na da ‘ya’ya maza uku, kuma dukkan su matuƙa jiragen sama ne.
“Duk wata sukan aiko masa da kuɗaɗe masu yawa a cikin kata-katan. To sai ƙawa ta ta shirya ita da wasu ƙawayen ta yadda za su sace kuɗaɗen.
“Wata rana matar dattijon ya tafi biki a Riyad, sai ƙawa ta ɗin ta kira wasu ƙawayen ta, ta ce su zo su kwashe kuɗin.
“Da su ka je sai suka wuce ɗakin da ake ajiyar kuɗin, su ka kwashe duka.”
Adama ta ce bayan ɓarayin sun fice, sai dattijon ya ce wa ƙawar ta, ya aka yi ɓarayin su ka samu makullin gidan har suka buɗe su ka shiga?
“A nan dai sai ƙawa ta kira ɓarayin ta ce to tsohon nan fa ya gane. Shi ne sai suka koma su ka ɗaure shi a kan kujerar keken da yake a zaune. Suka toshe masa baki da addugar amfanin mata lokacin al’ada, duk aka gudu har da ƙawar tawa.”
Adama ta ce wannan laifin ne ya sa aka biyo sawun su a daidai ranar da ita ma Adama ta je gidan waɗanda suka aikata laifin.
Ta ce asirin waɗanda su ka yi kisan tonu, ta hanyar mai aikin makullin da ƙawar ta ta kai aka yanka mata wani safaya. Ta ce shi ne ya bayar da shaidar cewa tabbas a rana kaza ‘yar aikin gidan mamacin ta je wajen sa ta kai makulli ya yanka mata.
Adama ta ce a ƙarshe dai ita an sallame ta, amma sauran su bakwai duk an yanke masu hukuncin kisa.