Ƴar Abba elmustapha ƴar shekara 12 ta haddace Alkur’ani cikin hotuna
Masha Allah diyar shugaban hukumar tace fina finai ta jihar kano Abba elmustapha Aisha almustapha (lateefa).
Shugaban abba elmustapha ya wallafa irin yadda yake cikin murna da jindadi na yana alfahari da yarsa akan wannan baiwa da Allah ya bata.
“Ina alfahari da ƴata A’isha abba almustapha (lateefa).
Ta haddace Alkur’ani mai girma tana da shekara sha biyu 12.
Allah ya kara albarka a rayuwarki yasa Alkur’ani ya zama gatanki.
Sai Godiya.”
Mutane sunyi martani na fatan Alkhairi ga abba elmustapha da yarsa akan wannan ni’ima.
@ali_dawayya yana cewa:
Masha Allah congratulations aysha Allah ya miki albarka yarda kika faranwa iyayenki rai kema Allah ya faranta miki Allah ya Kara karamiki rasarori a rayuwar ki duniya da lahira ameen ameen@abbaelmustapha1.
@saratudaso cewa take :
Congratulations.Allah yasa ta mori karatun ta cikin lfy.da nasan kwana.
@real_ibrahim_yala cewa yake :
Masha Allah, Allah Ya karawa Rayuwar ta Da sauran ƴaƴan Mu Albarka Amin..
@baballehayatu cewa yake :
Masha Allah.. congratulations..Lateefa Allah ya yi mata Albarka.
@alhajisheshe cewa yake:
Masha Allah Allah Yasa Haddarta Ta Amfanar Da Al,ummar Musulmi Da Mahaifanta Baki Daya.
@abdulamart_mai_kwashewa cewa yake:
Masha Allah. Congratulations to her.